WASU TSAGERU SUN SACE MANONA 13 A JIHAR LEGAS

0
935

Daga USMAN NASIDI..

WASU mutane su 20 wadanda ake tunani yan ta’adda ne sun kutsa wani yanki a Jihar Legas inda suka sace wasu manoma har su 13, wanda ya janyo mummunan tashin hankali a yankin gabashin jahar.
An ruwaito cewa yan ta’adda sun far wa wani guri da manoman suke zaune a kan hanyar Igbodu-Isowu a Ape yankin Legas, yan ta’addan sun yi basaja a cikin kayan sojoji.
Rohoton sun bayyana cewa wadanda aka sace sun hada da manoma guda 6, sai leburori guda 7. An bayyana wasu daga cikin wadanda aka sace kamar Oluwatoyesi Aboderin, da diyar \’yar uwarta \’yar wata 6, da wata mata manomiya Ogechi Maku.
An ce wadanda suka sace su, su 20 sun shigo yankin ranar Laraba suna harbe-harbe, bayan sun fito ta ruwa. Epe ta zama hanyar da \’yan ta’adda suke yawan bi, wani lokaci ma suna zuwa yin ta’asar su har yankin Ikorudu na jahar.
A watanni da suka wuce an bada rohoton cewa an sace wasu yan kwangila da suke aiki kan hanyar.
Duk da kokarin tsaurara matakan tsaro da Gwamnan jahar Ambode Akinwume yake , amma har yanzu abin ya ci tura.
Har yanzu yan sanda ba su ce komai ba kan faruwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here