Shirin Noma A Najerya An Girbe Amfanin Gona Mai Dimbin Yawa

0
1052

Rabo Haladu Daga  Kaduna

BINCIKE ya nuna cewa an samu ci gaba ta sosai ta bangaren harkar noma a wasu jihohin Najeriya, shekara da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin noman Shinkafa da Alkama da kuma bada tallafin bashi ga manoma ta hannun babban bankin Najeriya.
Inda Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu girbe amfanin goma masu dinbin yawa, musamman ma dai Shinkafa wacce akasari ita ce babban abincin al’ummar. A jihar Kebbi kadai an samar da Shinkafa fiye da ton Miliyan ‘daya da ake sasashe, a kadada fiye da Dubu 500 da aka noma a kananan hukumomi 10 a jihar.
Sai kuma wannan bai yi tasiri ba a wajen samun saukin farashin da wadatar abincin ga talaka, abin da wasu suka ta’allaka da yadda ake tsallakawa da abincin a domin sayarwa a makwabtan kasashe.
Malami a sashen nazarin tsimi da tattalin arziki na Jami’ar Usmanu dan Fodiyo ta Sakkwato, Rufa’i  Shehu, na ganin cewa sayar da abincin da ake nomawa a kasashen ketare ba zai haifar da ‘da mai ido ba ga Najeriya.
A nasu bangaren manoma na ganin wannan lamari a zaman ci gaba a sha’anin aikin gona da a baya ya tabarbare. Mohammed Lawal Mai Doki, ya ce ba sa fatar a ce abincin da suka noma ba ya fita zuwa wasu kasashe.
Yayin da Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta haramta tsallakawa da kayan abinci zuwa makwabtan kasashe. Takwaransa na Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, na ganin wannan ba matsala ba ce. Yana mai cewa idan farashin kayan abinci ya tashi mutane su kara nomawa, domin samar wa da wasu aikin yi.
A kwanannan ne dai mai taimakawa shugaban kasa a sha’anin watsa labari Mallam Garba Shehu, ya yi gargadin cewa Najeriya kan iya fuskantar matsalar karancin abinci ya zuwa watan Janairun sabuwar shekara, sakamakon fita da ake yi da dimbin da ake nomawa domin sayarwa a makwabtan kasashe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here