SIFETON \’YAN SANDA YA DAMU A KAN MUTUWAR JAMI\’ANSA 128

0
973

Daga Usman Nasidi

HUKUMAR \’yan sandan Najeriya na shirin fito na fito da yan baranda bayan \’yan sanda 128 sun rasa rayukansu cikin watanni 3 kacal
Sifeton yan sanda Ibrahim Idris ya ce  wajibi ne a kawo karshen wannan kuma a daina lalata dukiyoyin \’yan sanda.
Sifeto-Janar na yan sanda, Ibrahim Idris ya yi matukar nuna damuwarsa a kan mutuwan hafsoshin \’yan sanda.
\’Yan sanda sun bayyana ta hanyar kakakinsu DCP Don N. Awunah a ranan Laraba,Nuwamba 23 cewa sun rasa
maáikata 128 a watanni 3 da suka gabata.
Jawabin ta ce “Sifeto Janar na \’yan sanda, Ibrahim Idris NPM, mni, ya siffanta kisan jamián \’yan sanda a bakin aikinsu a matsayin babban abun damuwa. Wannan kisan gillan da \’yan daba ,\’yan baranda ke yi wa mutanen mu
wajibi ne a kawo karshen shi.
“Wani abun bacin ran shine yadda ake lalata kayan \’yan sanda da dukiyoyinsu. Wani sabon harin da aka kai a kauyen Dankamoji na karamar hukumar Maradu a Jihar Zamfara, Abagana a Jihar Anambra, Okrika a Jihar Ribas. Inda aka kashe \’yan sanda kuma aka lalata dukiyoyoinsu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here