KUNGIYAR KADUNA PROJECT TA KARRAMA SHUGABAN NUC FARFESA RASHEED

0
855
Daga Usman Nasidi

A wani taro da Kungiyar Kaduna Project ta gudanar, Kungiyar ta karrama sabon Sakataren Hukumar NUC ta kuma taya sa murna. An kuma kira sabon Sakataren Hukumar NUC din da ya zama mai gaskiya
da adalci.
Kungiyar ta Kaduna Project ta taya Farfesa Abubakar Rasheed murnar samun wannan matsayi na Shugaban NUC. NIC ta kuma taya Farfesa Umar Ibrahim murnar nada sa Shugaban laburare na Jami’ar Ahmadu
Bello ta Zariya.
A taron kuma dai, an karrama Shugaban Asibitin Koyon aiki na Jami’ar da ke Shika, an kira Shugabannin da suyi kokarin rike amana.
Har wa yau, Kungiyar ta taya ‘ya ‘yan na ta murna, ta kuma neme su da su zama masu
gaskiya da rikon amana.
Farfesa Rasheed wanda asalin ‘Dan Garin Makarfi ne na Jihar Kaduna, ya zama Shugaban Hukumar NUC mai kula da Jami’o’in Kasar nan a watan Agusta. Farfesa Rasheed tsohon Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano ne.
Amir Muhammad D. Muhammad ya kira Farfesa Rasheed ya rike gaskiya da amanar al’umma, ya zama mai amfani da basirar sa, ya kuma san cewa Ubangiji zai tambaye sa a Ranar Kiyama.
Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya yi godiya da kuma tabbatar da kamanta gaskiya a duk inda yake.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Mai Girma Yariman Zazzau, Mannir Jafaru da kuma Dan Masanin Zazzau, Falalu Bello da Farfesa Abubakar Sani Sambo da kuma wasu Manyan Malaman Jami’a da Shugabannin Al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here