JAM\’IYYAR APC NE TA LASHE ZABEN MAJALISAR TARAYYA A JIHAR LEGAS

  0
  967

  Daga USMAN NASIDI

  JAM\’IYYAR APC ta lashe zaben karashen da aka yi a Jihar Legas a karshen wannan makon. Dan takarar APC, Nuruddeen Akinwumi ne dai ya samu nasara a zaben da aka yi ranar Asabar din nan na kujerar majalisar tarayya.
  An gudanar da zaben ne a Gundumar Ifako- Ijaiye na Jihar Legas. Zaben dai karashe ne na dan takarar majalisar tarayyar kasa. Jami’in hukumar zabe na kasa wato INEC, Clement Aghatise, ya sanar da cewa dan takarar APC ne
  ya yi nasara a zaben.
  An sanar da sakamakon zaben ne cikin dare kamar yadda labarai suka nuna. Mista Clement Aghatise ya ce APC ta samu kuri’u 7640 a zaben, yayin da PDP kuma ta samu kuri’u 1771. Sauran ‘yan takarar irin su jam’iyyar SDP sun samu kuri’u 5 ne rak.
  Sai dai sauran jam’iyyun adawa sun ce ba su yarda da sakamakon zaben ba. Wani jami’in jam’iyyar ADC ya ce an tafka magudi a zaben. Shi dai Nuruddeen Akinwumi ya bayyanawa manema labarai cewa abu ya yi masa kyau. An dai gudanar da zaben ne bayan dan majalisar yankin ya rasu kwanaki.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here