Ba Mu Ji Dadin Hana Shigo Da Motoci Ta Kan Iyakokin Kasar Nan Ba-Yahaya Kega

0
998

Isah Ahmed Daga Jos

SHUGABAN kungiyar masu sayar da motoci ta kasa reshen Jihar Filato kuma shugaban kamfanin sayar da motoci na Kega Motors da ke garin Jos, Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana cewa ba su ji dadin matakin da gwamnatin Nijeriya ta dauka a \’yan kwanakin nan ba, na hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasar nan. Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Gaskiya Ta Fi Kwabo.
Ya ce a gaskiya mu masu sayar da motoci ba mu ji dadin matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na haramta shigo da motoci ta kan iyakokin kasar nan ba. Domin  motocin da ake shigowa da su  ta kan iyakokin Nijeriya ana biyan kudaden fiton su.
Ya ce kan iyakokin kasar nan, hanyoyi ne na shigo da kayayyaki don su wadata a cikin kasa kuma su yi sauki. To, yanzu an zo an ce an hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasar nan, kamar yadda aka hana shigo da shinkafa.
\’\’Wadannan abubuwa da gwamnati take yi a gaskiya tana kuntata wa al\’ummar kasar nan, musamman mutanen arewa. Domin yawancin harkokin da muka sanya a gaba ne ake takurawa. Wadannan abubuwa muna shigo da su
domin mu sami taro da sisi ta hanyar kasuwancinmu. Su mutanen kudu suna da mai  da tashoshin jiragen ruwa don haka  suna da abubuwan samun kudi. To dan wuraren da ake ci ake rage mana mu samu mu ci mu da
iyalanmu da mutanen da suke karkashinmu ana ta bi ana kullewa\’\’.
Alhaji Yahaya Kega ya yi bayanin cewa a gaskiya  ya kamata gwamnatin nan  ta sami masu shawara nagari, domin  wadanda suka kewaye shugaban kasa ba sa ba shi shawarwari nagari kuma mutane ne masu son kansu kawai.
Ya ce  kafin a zo a kafa wannan doka saboda matsalar tsadar canji ba a zuwa a sayo motocin nan sosai kamar yadda ake yi a da, domin  kashi 20 cikin 100  ne suke iya fita su sayo motocin nan. Ya ce to  yanzu da aka kawo wannan doka,  kamar an kulle kofa ne  kwata-kwata.
Ya ce wannan mataki  zai shafi  masu sayar da motoci kuma  zai shafi masu saye domin motocin za su kara tsada.  Don haka ya kamata gwamnati ta sake tunani kan wannan mataki da ta dauka na hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasar nan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here