\’Yadda Mijina Ya So Ya Kashe Ni Saboda Ba Na Haihuwa\’

0
1094

Rabo Haladu Daga  Kaduna

WATA mata mazauniyar kauyen Lakwushehe da ke Jos, a Jihar Filato Victoria ta kasance daya daga cikin matan da suka fuskanci musgunawa da kyama sakamakon rashin haihuwa.
Wannan baiwar Allah dai ta hadu da mijin da ta aura, a jami\’a, a inda kuma suka yi soyayya sannan daga bisani ta juye zuwa aure.
To amma farin cikin Victoria ya fara gushewa ne tun lokacin da ita da angonta suka je wurin likita kan batun haihuwa.
Mijin nata ya fara dandana mata kudarta bayan da likitan ya sanar da shi cewa Victoria ba za ta iya haihuwa ba.
Ga dai abin da Victoria ta shaida wa manema labarai
Lokacin da Maman Philip wadda ita ce mahaifiyar Victoria, ta ga \’yarta ta dawo gida, hankalinta ya tashi fiye da aniya.
Wasu alkaluma da hukumar lafiya ta duniya ta fitar a 2004 sun nuna cewa fiye da kaso 30 cikin 100 na mata masu shekaru 25 zuwa 49, na fama da wannan matsala.
Hukumar ta kara da cewa matan masu irin wannan matsalar sun fi yawa a yankin Afirka da ke kudu da Sahara.
A Najeriya kuwa kashi 10 cikin 100 na ma\’aurata ne ke fama da irin wannan matsala da Victoria John ta fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here