MAJALISAR DATTAWA ZA TA BINCIKI WASU KUDIN MAI DA SUKA BACE

  0
  813

  Daga Usman Nasidi

  A zaman ‘yan majalisar dattawan kasar nan, mambobin majalisar sun amince cewa lallai za a binciki wasu kudi da suka bata a gwamnatin shugaba Buhari.
  Majalisar ta ce bai kamata wasu kudi su rika bacewa daga asusun gwamnatin ba yayin da ake fama da rashin kudi a kasar.
  Sanata Dino Melaye ne ya kawo kudirin cewa ya kamata a duba wannan batu, Sanata Ali Ndume; shugaban masu rinjaye a majalisar kuwa ya mara masa baya.
  Sanatan ya ce kudi kusan Dala Biliyan 7 sun yi kafa daga NNPC da kuma NPDC.
  Majalisar za ta binciki shugaba Buhari da kuma ma’aikatar mai; Dokta. Ibe Kachikwu da kuma shugaban kamfanin mai na asa wato NNPC; Maikanti Baru. Majalisar Dattawar kuma za ta binciki Gwamnan Babban Bankin Kasa; Godwin Emefiele.
  Shugaban Majalisar Dattawar, Abubakar Bukola Saraki ya ce wasu na kokarin ganin yaki da cin hanci da rashawa da wannan gwamnati take yi bai kai gaci ba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here