\’Yar Tallar Ayaba Ta Shiga Hannun \’Yan Sanda Kan Satar Yaro

0
940

Musa Muhammad Kutama Daga Kalaba

WATA mata da take tallar Ayaba mai suna Chibuzor Eze  ta shiga hannu a garin Owerri, Jihar Imo sakamakon kamata da aka yi ake zarginta da sace  wani karamin yaro dan shekara uku,da haihuwa ta sayar wa wani mutum da shi kan kudi Naira 450,000.

Majiyar labarin mu ta ce matar ma kawa  ce ga iyayen yaron dukan su  mazauna  kauyen Umuifa ne , karamar hukumar Oru ta gabas. Majiyar ta  kusa da iyalan yaron ta shaida wa Aminiya cewa yaron yana ta wasansa ne a gidan  irin yadda yara suka saba yi misalin karfe takwas na safe kurum sai ta zo ta dauki yaron kamar wasa ta tafi da shi Owerri ta sayar .

Majiyar labarinmu ta ci gaba da cewa wanda ya sayi yaron ya bata awalajar Naira Dubu 150,000  daga bisani kuma ya cikata masa sauran yadda asirinta ya tonu ashe akwai wata matar daban da ta gane yaron ta ce ai wannan  dan makwabcina ne ya ya aka yi ya zo nan tsananta bincike da matar ta yi ne ta gano ashe sato yaron aka yi aka sayar ita kuma ta fallasa daga nan ne ba su yi kasa a gwiwa ba suka sanar wa \’yan sanda  a ka  kama su, mai sayarwa da kuma mai saye yanzu haka ana tsare dasu a ofishin \’yan sanda na Omuma.

Mai magana da yawun rundunar \’yan sandan Jihar Imo  Andrew Enwerem, da aka tuntube shi ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce wadanda ake zargi na hannu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here