Kanana Yara 400,000 Na Fama Da Yunwa A Nijeriya-MDD

0
902

Rabo Haladu Daga Kaduna

MAJALISAR Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa akalla kananan yara dubu dari hudu ne ke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki a shiyyar arewa maso gabashin Nigeria saboda rikicin Boko Haram.
Majalisar ta kuma ce kashi daya bisa biyar daga cikin su ka iya mutuwa a shekara mai zuwa.
Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar ta ce a wasu yankunan na jihar Borno da rikicin ya fi kamari, an lalata fiye da kashi daya bisa uku na hanyoyin ruwan sha da cibiyoyin kula da lafiya da kuma wuraren ba haya.
Majalisar ta ce ana samun karuwar cututtuka da suka hada da amai da gudawa da zazzabin cizon sauro, lamarin da ke kara jefa rayuwar kananan yara cikin hadari.
Akalla mutane dubu hamsin da biyar ne ke rayuwa a sansanin \’yan gudun hijira na garin Ngala a jihar Borno wadanda suka samu nasarar tserewa tada kayar bayan Boko Haram.
Hukumomin Nigeria sun kiyasta cewa akalla \’yan gudun hijira 3,000 ne suka kara zuwa sansanin na Ngala, cikin mawuyacin hali inda suke bukatar taimakon abinci.
Likitocin kasa da kasa da ke aiki a sansanonin \’yan gudun hijirar, sun bayyana cewa halin da yaran ke ciki ya munana, ya yin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kananan yara dubu saba\’in da biyar ne ke fama da rashin abinci, kuma matukar ba a dauki matakin gaggawa ba, yaran na cikin barazanar rasa rayukansu cikin watanni masu zuwa.
Fiye da shekara guda kenan gwamnatin da dakarun soja ke nanata cewa sun kusan kawo karshen tada kayar bayan \’yan ta\’addan, kuma dubban mutane su na komawa garuruwansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here