Sakataren Munazzamatul Islam Ya Nemi A Yi Wa Najeriya Da Shugabanninta Du\’a\’i

0
990

Musa Muhammad kutama Daga kalaba

MAKARANTAR Islamiyya ta Nurul Huda da ke layin bagobiri Unguwar Hausawa Kalaba ,Jihar Kuros Riba ta bi sahun takwarorinta na sassan duniya daban daban wajen gudanar da bikin maulidi, shekaranjiya daliban makarantar mataki daban-daban ne suka yi karatun daga cikin Alkur\’ani mai girma da kuma tabo wasu kadan daga  cikin tarihin fiyayyen halitta Manzon tsira s.a.w. Bayan da aka kammala taron sakataren yada labarai na kungiyar  munazzamatul  Islam ta kasa reshen Jihar Kuros Riba  Alhaji Lawal  Ibrahim Isah ya bukaci ilahirin makarantun islamiyya da ma al\’ummar kasa baki daya da su yi amfani da wannna lokaci na maulidi wajen yi wa kasa addu\’a da kuma shugabanninta .

Ya ce “ina kira ga al,ummar musulmin Nijeriya da su yi amfani da alfarmar wannan wata na haihuwar fiyayyen halitta da ake ta bukukuwan tuna zagayowar ranar haihuwarsa su dukuma da yi wa kasa da shugabanni addu\’a da kuma sauran kasashen da ake tsangwamar musulmi baki daya”.Ya kara da cewa bai kamata ba “matsayinmu na musulmi a ce wasu daga cikin mu suna yi wa juna gani na fifiko suna ganin cewa su, su ne cikakkun musulmi wasu kuwa ba haka ba ne suna bata akidojin su “.hakan babu abin da zai haifar face rabuwar kawuna .

Da yake yin tsokaci kan matakin hana yin wa\’azi ba lasisi da wasu gwamnatocin kasar nan da ke arewacin Nijeriya suka dauki mataki sakataren watsa labaran kungiyar  munnazamatu Alhaji Ibrahim Isah ya ce daukar matakin matukar zai kawo zaman lafiya da kuma kawar da fitina ya dace a dauka “amma bai kamata ba a ce dakatarwar wani bangare a ce yana yin murna da hakan ba don an hana wasu”.injishi

Da aka tambaye shi gaskiyar furucin da aka ce ya yi na cewa idan aka kuskura a kasar nan wani ya taba dan darika to za su fanshe a zaben 2019 idan Allah ya yi nufin mu da gani malamin ya kara da cewa “ falillahil hamdu abin da nake cewa taba dan darika ai ba za ka taba mutum ba tare da hujja ba ,idan an taba dan darika don a yi masa zalunci idan lokaci na zabe ya zo \’yan darika suka kaurace masa ta yaya za a yi a ce wannan dan takara zai ci zabe lura da cewa mafi yawancin kuri\’u na fitowa ne daga wurin \’yan darika”.

Ya yi fata duk wani shugaban da ba  dan darika ba ne ya hau   mulki to ya yi wa \’yan darika adalci a kodayaushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here