SOJOJI SUN CETO WASU MATA DA YARA 605 DAGA DAJIN SAMBISA

0
1087

Daga Usman Nasidi

RUNDUNAR sojojin Najeriya na ci gaba da aikinsu a dajin Sambisa don banbare \’yan ta’addan Boko Haram wannan ya kai su ga
ceto mata da yara 605.
Dajin ya kasance matattara na \’yan ta’adda a arewa maso gabas tare da \’yan matan Chibok da aka rahoto cewa suna boye a gurin.
Leo Irabor wanda ya kasance kwamandan tawagar yay i Magana a lokacin wani taron manema labarai a hedkwatan yanki na 7 na Operation Lafiya Dole a Maiduguri inda ya tabbatar da ceto matan da yaran.
Ya bayyana cewa rundunar sun ci gaba da samun nasara a kokarinsu na shiga dajin Sambisa.
Ya ce \”an ceto maza manya 69, maza yara 227 da kuma yara mata 129, lokacin aikin tsakanin 7 ga watan Disamba da 14 ga watan Disamba.
“Wadanda aka ceton na karkashin kulawarmu don ci gaba da bincike da kuma tambayoyi.
“Kan aikin, rundunarmu sun maida hankali gurin shafe \’yan ta’addan daga inda suka boye. Zan iya fada maku cewa an riga da an fara nasara kan \’yan ta’addan.\”
A halin da ake ciki, shugaban hafsan soji Tukur Buratai ya tabbatar wa \’yan Najeriya cewa ta’addanci a arewa maso gabas zai zo karshe a 2017.
Buratai, lokacin da ya kai ziyara ga bataliya 81 a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba, yay i alkawari ga dukkan sojojin da ke yaki da \’yan ta’adda cewa za su koma bariki a shekara mai zuwa. Ya ce hakan zai faru da zaran an gama yaki da \’yan ta’adda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here