Sun Yi Alkawarin Aiki Tare Da Hukumomin Tsaro Don Inganta Rayuwar Al\’umma

0
964

Jabiru A Hassan,  kano.

WANI jigo  a kungiyar banga ta kasa watau VGN  Malam Muktar Abdullahi Ungogo  ya yi alkawarin yin aiki da hukumomin tsaro domin inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano da ma kasa baki daya.
Ya yi wannan bayani ne a zantawarsa da manema labarai a Kano ciki har da wakilinmu, inda ya ce ya zamo wajibi a rika taimaka wa jami\’an tsaro wajen tabbatar da ganin ana cimma kyawawan nasarori ta fuskar tsaro musamman ganin irin kokarin da gwamnatoci ke yi na inganta tsaro  da samar da zaman lafiya a wannan kasa tamu.
Ya ce da yardar Allah za a sami ingantuwar al\’amura a Nijeriya  saboda ganin yadda ake kokari wajen daidaita lamuran tsaro a kasa, sannan ya jinjina wa gwamnatin Jihar Kano saboda daukar matakan da take yi ta fannin tsaro da wadata jami\’an tsaro da ingantattun kayan aiki.
Malam Muktar Abdullahi Ungogo ya kuma yaba wa kokarin kungiyar ta VGN bisa jagorancin Alhaji Dokta Ali Sokoto  wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kowane lungu na kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here