Dalilina Na Yin Bincike A Kan Addinin Musulunci- Farfesa Egody

  0
  1193

  MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga kalaba

  A makon da ya gabata ne Hukumar hadin kan limamai da malaman addini ta Jihar Kuros riba ta gudanar da lacca mai taken hadin kan Musulmi da kuma mu’amala tsakanin sauran addinai.

  Cikin wadanda suka samu damar halartar laccar har da Farfesa Egody Uchendu, malama a Jami’ar Najeriya da ke Nsukka Jihar Enugu. A yanzu haka tana gudanar da bincike kan rayuwar Musulunci da ta Musulmi a Jami’ar Kalaba. Ko me ya sanya a matsayinta na Kirista ta zabi ta yi bincike kan wannan maudu’i? Wakilinmu na kudanci musa Muhammad kutama  ya gana da ita kuma ga yadda tattaunawarsu ta kasance:

  GTK:Wace ce Farfesa Egody?
  Sunana Farfesa Egody Uchendu ta Jami’ar Najeriya Nsukka, sashen tarihi da nazari kan harkokin kasa da kasa amma yanzu ina zama malama ta wucin gadi don ci gaba da bincike a Jami’ar Kalaba sashen tarihi da nazari kan harkokin kasa da kasa.
  Mun samu labarin cewa kina yin nazari tare da gudanar da bincike kan Musulunci da kuma zuwansa Jihar Enugu, haka ne?
  Farfesa Egody:Eh!, wanda ya gaya maka da gaske yake, da gaske ne ina gudanar da wannan bincike ne da nazari hususan kan Musulmi, Musulunci a gabashin Najeriya.
  GTK:Tun yaushe kika fara wannan bincike?
  Farfesa Egody;Tun a shekara ta 2009, lokacin zuwana na farko Kalaba ke nan. ’Yan kwnaki kadan ma na yi na koma, daga nan kuma ban sake zuwa ba har sai da wannan damar ta samu in zo Jami’ar Kalaba aiki na wucin-gadi don ci gaba da bincike. Watanni biyu ke nan ma da zuwana, shi ne sai na ga ashe wata dama ce ma gare ni, na ci gaba da yin bincikena; tunda a can ma akwai dinbin al’ummar Musulmi.
  GTK:Me ya jawo hankalinki kike yin wannan nazari da kuma bincike?
  Bukatar son in san yadda rayuwar Musulunci da Musulmi take ce ta sanya. Abin farin ciki ma, limamin da na fara samu a can wajenmu yake, ka san ba kamar lokacin da na zo ba shekaru 7 da suka gabata. Wato abin da na lura a Musulunci shi ne, farko rashin fahimtar da wadanda ba Musulmi ba suke yi wa addinin da kuma masu shi, tun daga nan ne na kuduri aniyar yin nazari tare da binciken dalilan da suka haifar da hakan. Ka ga ni ’yar kabilar Ibo ce kuma Kirista, ka ga bisa al’adarmu yadda muke gaisawa da juna muna yin masafaha ce. Misali, idan ka hadu da wani babban mutum haka, hanyar da za ka mutuntashi a gaisuwa ita ce yin masafaha, sannan kuma akwai rungume juna amma hakan akwai zabi; babu tilas, duk wanda ka zaba shi za ka yi. Yanzu na fahimci tsakanin Musulmi su abun ba haka yake ba, addinin Musulunci ya hana mace ta yi masafaha ko namiji ya yi masafaha da mace tun daga nan na dauki darasi da dadewa na daina yin masafaha da namiji.
  Makasudin binciken nawa ma shi ne kan rayuwar Musulunci da ta Musulmi, wato wani abu ma da ya kara sanya mini faraga da farin ciki a wannan bincike shi ne, sama da shekara 15 yanzu ni ce mai kula da wani darasi a tsangayar karatunmu kuma mun fara ne da darasi kan addinai kafin daga bisani a sauya akalar darasin zuwa addinai a Afirika ta yamma kuma ka ga duk da haka karkashin darasin ni ce nake koyar da darasin addinin Kirista kuma ni ce ke koyar da na addinin Musulunci; kai har ma da addinin gargajiya duka ni ce ke karantarwa. Ta nan ne ma na samu damar samun duk wasu bayanai na addinan, har ila yau ta hana nake nuna wa dalibai yadda mabiya addinai daban-daban suke a nahiyar Afirika da ma sauran sassan na duniya.
  GTK:Farfesa, lura da bayanai da kuma fahimtarki, ya za ki kwatanta mu’amala tsakanin mabiya addini Musulunci dana Kirista har ma da masu addinin gargajiya?
  Farfesa Egody: Ah! Tarihin Najeriya daga 1940 zuwa yanzu, hakika ya bambanta a dan tsakanin nan. Na lura akwai tsangwama da kyarar juna a wasu lokutan ma da rikici na addini. Hakan ya samo asali tun daga shekarar 1940. Daga 1980 zuwa lokacin nan da muke tattaunawa kuma ana fama da rashin yarda da juna da kuma sauran rikici na addini da na kabilanci. Na yi matukar farin cikin ji daga bakunan malamai a jawaban da suka gabatar kan mece rayuwa da kuma yadda ta kamata ta kasance, lura da duniyar na zamanta kadan ne, to ashe tun da haka ne babu abin da ya fi mu zauna da juna lafiya. Ni ban ga dalilin da ya sa za mu rika far wa juna ba, ba mu iya hakuri da juna. Jiya na yi matukar mamaki da na kunna akwatin talabijin, na ji labari wai a Kano, an kashe wata mata da ta yi batanci na addini, an ce ta yi batanci ga Manzo kamar yadda na ji wani daga cikin malamai a makalarsa da ya gabatar, ya ce idan ba ku mutunta addininsu ba su ma ba za su mutunta naku ba. Na ji dadin jin haka, maimakon haka, kamata ya yi a nun masu mafi nagartar Musulunci. Ina mu’amala da Musulmi har yanzu. Matsalar da nake lura da ita, ita ce yaushe ne Musulmi za su nuna nagartar Musuluncin, tunanina abin da nake son na gani ke nan har yanzu ba fa’ida ba ce a ce ba za mu iya magance matsaloli tsakanin Musulmi da Kirista ba. Ina ganin idan ana rika hada mahalara irin wannan da kuma rika yin taron kara wa juna sani, hakan zai taimaka matuka gaya a samu fahimtar juna a warware matsala tsakani.
  GTK:Matsayinki na mai bin addinin Kirista, ko za ki bayyana mana irin taki fahimtar game da Musulunci da Musulmi?
  Farfesa Egody:Dukkaninmu mutane ne k uma Allah ne Ya halicce mu.  Idan muka duba yadda ma Allah Ya yi mu, zamanmu na duniya za mu ga wasu fararen fata ne wasu kuma bakake, wasu jajaye wasu kuma gajeru wasu dogaye, abin da nake son cewa shi ne, kamar yadda aka halicce mu jinsi da kala daban-daban; haka ma addinanmu sun bambanta. Musulmi Muslmi ne ko ta hanyar kaddara ko kuma ta shiga addinin, haka ma Kirista yana addinin ne bisa kaddara, wasu kuma sun karbi addinin Kirista ne bisa radi na kashin kansu, kamar yadda nake Kirista kai kuma Musulmi muke, tattaunawar nan. Kada mu bari wani abu dangin son zuciya ya raba tsakaninmu.
  GTK:Ko akwai wani sako da kike son isarwa ga alumma?
  Farfesa Egody: Na yi farin ciki da na samu damar halartar wannan fadakarwa da lacca da aka gabatar, musamman makalolin da malamai suka gabatar kan zamantakewa, na kuma karu da irin yadda na ji rayuwar Musulunci da ta Musulmai.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here