Jami\’an Kwastan Sun Yi Wawan Kamu A Imo

0
1003

 

Musa Muhammad Kutama Daga Owerri

HUKUMAR  hana fasa kauri ta Nijeriya sashen kula da ayyuka na kasa rukunin C. dake owerri,jihar Imo ya bankado tare da damke wasu motoci da aka tsangare su da buhunan shinkafa ‘yar waje tare da buhu nan tabar wi-wi kana kuma da gurbataccen danyen man fetur dama sauran karikitan da gwamnati ta hana a  shigo da su cikin kasa .

Da yake tabbatarwa manema labarai kamen da akayi shugaban shiyyar   rukunin  Mohammed Uba Garba, ya ce motar motar da jami’an sa suka kama ya bayar da lambar motar kamar haka   GBB 85 XA, ake zargi ta dauko jirkitaccen man fetur an kamata a hanyar Aba zuwa Owerri. Ya ci gaba da cewa “an gano wata hikima da masu fasa kwaurin sukayi ta yin wani tankin zuba mai sain suka lullubeshi da wasu buhunan kayan gurbataccen  abincin kaji guda 256 da nufin su yi badda bami a ce sharace suka dauko zasu zubar.

Mohammed Uba ya ce direban motar mai suna  Chibuzor Njoku da aka kama za,a mika shi ne ga jami’an tsaro na sibil difens domin fuskantar hukunci na gaba. Haka nan kuma jami,n hana fasakwaurin ya kara da cewa akwa mata motar ma mai lamba 1 X 40” da daya kuma mai wannan lambar  MRKU 254564, aka loda masu tabar wi-wi buhuna   1,017  da aka kiyasta kudin su Naira 16,000,000 yayin da suke kan hanyar su ta zuwa shagamu.Yace direban motar mai suna  James Idoko, wanda domin ya kubuta ya shara masu karya cewa shi dalibi ne na wata makaranta sun kama shi a tare da shi wasu jabun takardu na yarda da hukumar kwastan ta yi masa na ya  rika shigo da kaya .Bayan da  wanda ake zargi ya tabbata ba shi da mafita ne ya yi kokarin ba su cin hanci na naira dubu 350,000 domin su sake shi yanzu haka tabar wi-wi da aka kama shi da buhunan ta ana jira hukumar yaki da hana shan miyagunn kwayoyi su kiyasta kudinta.

Bugu da kari ita kuma motar da ta dauko buhunan shinkafar kasar waje motar na da lamba kamar haka KRV 238 XB ta dauko shinkafa ce mai dauke  da tamburan kasuwa daban-daban har buhuna  725  kuma abayanan kayan da takardar kayan ta nuna da kwastan suka kama ya nuna an biya kudin fito naira 24,650,000.kuma an shigo da kayan ne ta barauniyar hanyar Kalaba zuwa kamaru ,jamhuriyar kamaru.wanda yab daukom kayan da aka kama mai suna   Fredrick Eze ya ce shi wakilin mai kaya ne amma duk da haka an tsare shi har sai mai kayan yazo. Inji jami,in kwastan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here