Rugujewar Kasuwa Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mata Biyu

0
846

Musa Muhammad kutama Daga Uyo

AKALLA wasu  mata biyu aka ce sun rasa rayukan su yayin da wasu mutane goma sha bakwai kuma suka ji mummunan rauni sakamon faduwar ginin  kasuwar Urua Edet-Obo da ke yankin   Ikot Akpatek,karamar hukumar   Onna, jihar Akwa Ibom .wakilinmu na kudanci ya tunatar goma ga watan Disamba da muke ciki ne rufin ginin wata majami’a ta reigners da ke Uyo hedkwatar jihar ya fado ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da metan bisa kiyasi.

Kwamishinan ,’yan sandan Jihar Akwa Ibom Murtala Mani ne ya tabbatar da afkuwar hakan ga manema labarai a Uyo jiya Litinin ya ce “katangar kasuwar  ce ta ruguzawa wasu mutane ciki har da wasu mata biyu suka rasa rayukan su yayin da wasu mutane goma sha bakwai aka kiyasta sun ji mummunan rauni na faduwar katangar.

Ya kara da cewa wadanda suka ji rauni kuma an kai su  asibiti, domin ba su kulawar gaggawa, yayin da   gawarwakin matan kuma an kai su   asibitin  Eket, majiyatan na samun sauki kamar yadda kwamishinan ya tabbatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here