Aiwatar Da Kyawawan Dabi\’u Ne Za Su Sanya A Fahimci Musulunci -Farfesa Sani Zahraddeen

  0
  1058

   

  KWANAN baya Majalisar Limamai Da Malamai ta jihar Kurosriba ta gudanarda taron lacca a Kalaba, mai taken: “Rayuwar musulunci da musulmi da ’yan matsalolin da za su tunkara domin warware su da kuma dangantaka  da mu’amala tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba, yadda addinin musulunci ya tanada,’’ da aka yi a dakin taro na karamar hukumar birnin Kalaba. An gayyato manyan baki daga ko’ina cikin kasar nan, musulmi da wadanda ba musulmi ba. Farfesa Muhammad Sani Zahradeen, Babban limamin Kano shi ne ya wakilci Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammad Sanusi na biyu. Bayan  an tashi  daga  taron wakilinmu na kudanci musa Muhammad kutama ya  tattaunada babban limamin.   Ga yadda hirar ta kasance:

   

  GTK: Farfesa Babban Limamin Kano  Me ya kawo ka Kalaba?
  Sheikh Muhammad Sani: Babban abun da ya kawo ni Birnin Kalaba babban birnin jihar Kuros riba shi ne, Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu, wannan kungiya ta Majalisar Limamai Da Malamai na wannan jiha ta gayyace shi taron da za su tara dukkan limaman Akwa Ibom da na Kurosriba domin a tattauna yadda za a samu zaman lafiya tsakanin musulmi su kansu da kuma wadanda suke ba musulmi ba a wannan jiha. Mai martaba Sarki ya samu wannan gayyata sannan ba ya nan ya yi tafiya, ba ya kasar ya ce  ni limamin  Kano in wakilce shi, shi ne na zo,  kuma an yi wannan taro cikin nasara, cikin nishadi,  in sha Allahu wannan abu ne na tarihi.
  GTK: A makalolin da aka gabatar, tarbiyya na daya daga cikin mataki na farko da za a ,bi wadanne hanyoyi ne Sheikh yake gani za a bi cikin sauki a cusa wa matasa tarbiyya?
  Sheikh Muhammad Sani: Babbar tarbiyya da za a cusa wa mutane, musamman matasa samari da ’yan mata, ita ce su tsaya su san meye ma musuluncin, su nemi ilmi kowane iri ne, kamar yadda marigayi Malam Sa’adu Zungur yake cewa, “Mu dai ilmi muka tambaya ko a Landan ko a Arebiya.” Manufa ko ilimi irin wannan na zamani da ake yi ko kuma ilimi na addini, duk irin wannan abu ne wanda yake muhimmin gaske,to su tashi tsaye kawai su nemi ilmi. Ubangiji (SWT) Ya fada wa Annabi (SAW) cewa, ka ce, Ubangiji Ka kara min sani, kuma Manzon Allah (SAW) yana da sani, kuma Ubangiji Ya sanar da shi abubuwa da yawa, amma duk da haka Ubangigji ya ce, ka ce, Allah Ka  kara min ilimi. Saboda haka wajibi ne ga dukkan wani musulmi ya tashi tsaye ya nemi ilmi na wannan zamani ya kuma nemi ilmi na addini, domin irin wannan ne shi Mai martaba ya sanya kwamitoci har guda uku da taimakon wadansu malamai na jami’a a nan Jami’ar Bayero da kuma malamai na cikin gari sanannu domin a tattauna wadannan al’amura, musamman ilimin yara da ilmin zamani. Yaya musulmi suke baya a wajen harkar ilimi, kwamitinmu ke nan.  Na biyu, kwamiti ne na duba harkokin aure. Yaya za a yi musulmi da musulma su zauna lami-lafiya a gidajensu. Sannan kuma sai tarbiyyar yaransu a bisa hanyar addinin musulunci. Na uku kuma shi ne, An fahimci cewa musulmi suna baya wajen harkokin tattalin arziki da ciniki da sauransu. Yaya za a yi a bunkasa wannan, a sanar da su cewa musulunci fa bai ce a zauna haka ba, kuma a fadakar da jama’a, a jawo hankalinsu wajen bayar da Zakka, yadda za a taimaka wa mara karfi.
  GTK: sukuma iyaye fa wacce irin rawa ya kamata su taka wajen tarbiyar ’ya’yansu, musamman shigowar kafafen sadarwar na zamani da ake zargin suna dada taimakawa wajen cusa wa matasa bakaken akidu?
  Sheikh Muhammad Sani: kwarai da gaske, su kansu iyaye su ma su fara gyara kansu, don shi yaro idan ya tashi abun da ya gani ana yi a gidansu sau da yawa shi yake tashi da shi, iyaye su tashi haikan  su gyara kansu wajen tarbiyya irin ta musulunci,sannan kuma wadannan kafafen sadarwa na sada zumunta  na zamani da ka fada, irin su intanet da was’af, iyaye  su rika kokarin sanin shin  su waye abokan ’ya’yansu ne, wance wacece kawarta? saboda a nan yawanci daga wajen kawaye ake koyon abubuwan da ‘yan mata suke koya, wadansu samari kuma daga abokansu ne, saboda haka a rika tabbatar da cewa yaransu suna tare da mutane na kirki. Malamai suna fadi,  kada ka tambayi halayyar wani mutum, amma ka dubi abokinsa, yadda abokinsa yake, to haka yake. Saboda haka yadda kawa take, haka ita ma daya kawar  take. Saboda haka a kula da su waye ne samarin ’ya’yanmu mata da kuma su waye abokan ’ya’yanmu matasa da suke hulda da su ta yau da kullum.
  GTK: Ana zargin kafafen yada labarai na yammacin duniya da  kururutawa tare da bata sunan musulnci da musulmi wajen ta’addanci, wane karin bayani za ka yi?
  Sheikh Muhammad Sani: Ai abun dama ba  haka yake ba, kamata ya yi  su musulmi su rika tabbatarwa sun tsaya ka-in-da-in sun yi wannan musulunci daidai gwargwado, saboda idan ba haka ba sau da yawa idan an yi wani mummunan al’amari sai a ce musulunci ne, ko a ce kaza, kuma dama abu ne wanda aka saba, an dade ana samun rigima, akwai wani rashin fahimta tsakanin wadanda suke musulmi da wadanda ba musulmi ba.To musulmi su fito fili su rika gaya wa ’yan uwansu musulmi meye musulunci, kuma su yi kokari su yada abubuwa na musulunci masu kyau, irin kula da dangi da kula da makwabci da yin sadaka da taimakawa, idan kana da hali ka rika ba dan uwanka abun da ya dace ka rika bashi, to wadannan abubuwan da ake yi na alheri su ne za su iya sanya wadanda suke ba musulmi ba su ga lallai da akwai wani abu a musulunci da ya fi abun da ake cewa ana yi .
  GTK: Wace shawara za ka bayar yadda wadanda ba musulmi ba za su fahimci tsantsar gaskiya addinin musulunci?
  Sheikh Muhammad Sani: Ai shi ne abun da na gaya maka cewa ka-in-da-na-in su yi wa jama’a bayani kan mene ne musuluncin kansa, ba wai kawai a barshi kara zube sai yadda mutane suka gani ba, a’a da kyakkyawan hali da yawa mutanen da suka musulunta a nan kasashen Afrika ta yamma, ba wai ta hanyar  yaki suka musulunta ba, a’a ganin yadda musulmi, musamman ‘yan kasuwanmu suke shiga dazuzzuka, suke shiga garuruwa, suke yada musulunci, wato yada musulunci ta irin halayya ta musulunci, idan an yi hulda da su a ga mutane ne masu gaskiya, idan sun yi hulda masu rike alkawari ne,  ba su da wani mummunan hali wanda za’a kyamace su, to abun da yakamata ke nan  musulmi su yi.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here