Dalilin Da Ya Sa Ban Halarci Auren Zahra Buhari Ba- Sarkin Maradun

0
1759

Daga Mustapha Imrana Abdullahi

Mai martaba sarkin Maradun da ke cikin Jihar Zamfara ya bayyana dalilin rashin halartarsa wurin daurin Auren yar shugaban kasar tarayyar Najeriya Zahra Buhari.

Shi dai wannan aure na yar shugaba Muhammadu Buhari ya dade yana zama wani kace nace a bakunan yan kasa, wannan ne ma yasa sanannen sarki na kasar Maradun baii daya dole tasa ya yi watsi da zuwa wajen auren lamarin da aka bayyana da ake zargin cewa umarni ne daga gwamnan jihar

Wadansu manema labarai da suke kusa da fadar mai nisan yan kilomitoci kalilan daga birnin Gusau, fadar ta Maradun majiya ta shaida mana cewa shi Sarkin na Maradun shi ne zai bayar da auren Zahra ga dan kasuwa mai tarin biliyoyi da ya fito daga kasar Barno wato Muhammad Indimi.

” Amma yana cikin tafiya zuwa Abuja ,sai aka kira shi a waya inda aka umarce shi davya tsaya Kaduna. An shaida mana daga majiya mai tushe cewa kiran daga wurin gwamnan Zamfara ya fito inda aka bashi umarnin yaje ya halarci wani taro lamarin da ya zamar masa dole ya yi watsi da zuwa Abuja domin kare rawaninsa na sarkin Maradun,” inji majiyar

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa rashin halartar sarkin tasa dole aka canza tsarin ba kamar yadda aka shirya can baya ba, wanda a dole aka sa Sarkin Fulanin Daura domin ya aiwatar da aikin da aka shirya sarkin na Maradun zai yi na bayar da amarya kamar yadda addinin musulunci ya shimfida.

An yabbatar da cewa sarkin Maradun yana kusa da iyalin shugaban kasa Buhari “saboda ko a kwanan baya ma shi ne ya bayar da Auren Halima Buhari lokacin da aka aurar da ita.

Ita dai Halima yar shugaban kasa ce da ya haifa da wata matar daban.

Tun lokacin da aka yi wannan aure na Zahra Buhari dai ana ta zargin cewa lallai dangantaka ta yi tsami tsakanin gwamnan Zamfara da kuma iyalin shugaban.

Tun da dadewa dai ake ta yada batun cewa gwamnan Zamfara na son Zahra Buhari kuma kafafen labarai na cewa batun auren ma zai zama gaskiya.

Amma sai batun soyayyar ya zama ya canza haka kawai inda aka bayyana dan gidan hamshakin dan kasuwa Indimi da cewa shi ne angon Zahra Buhari.

Ta yuwu hakan ne yasa gwamnan ya dan kadu wanda masu sa idanu suka rika ruwaito wa cewa sam gwamnan bai halarci auren ba ko kadan a duk lokacin da aka yi shi a Abuja.

Kuma ya zuwa yanzu babu wani dalilin da aka bayar na ko me yasa bai halarci auren ba taron auren da ya hada kusan kowa a duk cikin kasu ruwa da tsaki musamman a lamarin mulkin kasar.

Duk kokarin da muka yi na tuntubar mai taimakawa gwamnan Zamfara a harkar yada labarai lamarin ya ci tura saboda har sakon karta kwana an aika amma nema bai cimma samu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here