Ya Shawarci \’Yan Siyasar Yammacin Kasashen Afrika

  0
  849
  Jabiru A Hassan, Daga Kano.

  AN shawarci shugabannin kasashen  yammacin  Afirka da su rika mutunta tsarin mulkin dimokuradiyya domin kaucewa jefa kasashen su cikin rikice~rikice wanda hakan ke jawo koma baya a nahiyar.

  Wannan shawara ta fito ne daga wani tsohon dan majalisa a jamhuriya ta biyu Alhaji Ahmadu Abdullahi Badume a zantawarsu da  Gaskiya Tafi Kwabo, inda ya bayyana cewa yana dakyau  duk shugaban da ya fadi zabe to ya mika mulki ga wanda Allah ya baiwa nasara maimakon kin amincewa da sakamakon zaben da aka bayar domin tabbatar da zaman lafiya a kasashen su.

  Alhaji Badume ya bada misali ga yadda tsohon shugaba Jonathan ya mika mulki ga shugaba Buhari da yadda shugaban Ghana yake shirin mika mulki ga wanda ya kayar dashi zabe, inda kuma ya nemi shugaba Yahaya Jammeh na Gambiya da shima ya mik amulki ga zababben shugaban kasar da al\’umar kasar suka zaba domin tabbatar da zaman lafiya a kasar kamar yadda ake bukata.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here