An Kama Matashi Mai Lalata Da Dabbobi Don Kada Ya Kamu Da HIV

0
1507

Musa Muhammad Kutama Daga Kalaba

WASU matasa da suka harzuka a kasar Kenya sun damke wani matashi dan kasar mai kimanin shekara 23 da haihuwa mai suna Otieno Jalango, suka mika shi ga basaraken su Jim Kawa     saboda samunsa da laifin yin  jima’i da akuyar makwabcinsa.Kamar yadda wata kafar yada labarai da ake wallafawa ta intanet ta ruwaito wannan jarida ita kuma ta kalato, Jalango,dubunsa ta cika ne a kudu maso gabashin Muhuru Nyatike ,Migori.

Jaridar mai suna edaily  kamar yadda ta ruwaito bayan matashin ya shiga hannu ne ya furta da bakinsa ba tare da an tilasta masa ba ya ce ya yanke shawarar rika tarawa da dabbobi ce “domin gudun kada ya harbu da cutar mai karya garkuwar jiki kanjamau jima’i da dabbobi ya fiye masa “inji shi.

Matashin bayan an mika shi ga basarake Jim Kawa ya ce “hakika yana saduwa da jakuna da kuma tumaki har ma da karnuka”.inji basaraken.kamar yadda aka ruwaito

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here