Matsalar Boko Haram: Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Ofisoshin ‘Yan Sanda 25 Makarantu 25 A Adamawa –Sakataren Gwamnati

0
862

Daga Muhammad Shafi’u Saleh Da Ladan Habibu
GWAMNATIN tarayyar Nijeriya ta tabbatar da cewa za ta gina ofisoshin ‘yan sanda 25 da makarantu 25 a yankunan da rikicin boko haram ya yi wa lalata a jihar Adamawa.
Sakataren gwamnatin tarayyar Babachir David Lawal, ya bayyana haka a jawabin da ya gabatar wajen bukin addu’o’in shigowar kirsimati
(Christmas Carol Service) da aka yi a cocin St. Theresa’s Cathedral da ke garin Jimeta fadar jihar Adamawa.
David Lawal ya ci gaba da cewa wani babban abu da gwamnatin tarayya ta maishe da hankali a kai shi ne tabbatar da tsaro da tsare dukiya da
rayukan jama’ar yankin, da kuma bunkasa tattalin arziki a yankin baki daya.
“yanzu haka gwamnatin tarayya ta gyara da sake gina wasu makarantu da ba su gaza 25 da rikicin boko haram ya lalata a kananan hukumomi bakwai na Adamawa ba. “har yanzu gwamnatin tarayya ta kammala shirin gina wasu ofisoshin ‘yan
sanda 25 a yankin da rikicin ya shafa” inji sakataren gwamnatin tarayyar.
Ya ce kasafin kudin shekarar 2017 da shugaban kasa ya gabatar wa majalisun tarayyar kasar yana kunshe da hanyoyin farfado da tattalin
arziki da ci gaban al’ummar kasar ne.
Ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma amince da gyaran wasu hanyoyin gwamnatin tarayyar guda hudu duk a cikin kasafin kudin na bana.
Sakataren gwamnatin tarayyar ya bayyana hanyoyin Yola-Mubi, Mararaba Mubi, Gwoza a jihar Borno, da Numan Cham a jihar Gombe da kuma Numan- Jalingo da cewa kudin aikin gyara su na cikin kasafin kudin 2017.
Da yake gabatar da jawabi a taron, shugaban majalisar wakilai ta kasa Yakubu Dogara,  ya tabbatar da cewa za su hada hannu a daukacin
bangarorin gwamnati domin ciyar da kasar gaba.
Kakakin majalisar wakilan ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da bai wa gwamnatin tarayya da sauran ‘yan siyasa da ma shugabannin
addinai goyon baya, da kuma bin doka da oda.
Shugaban Cocin St Theresa Cathedral Bishof Dami Mamza, ya hori malaman addini da a kowane lokaci su tabbatar sun koyar da jama’a abubuwan da ya dace domin tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a kasar.
Wasu daga cikin manyan bakin da suka halarci taron sun hada da mataimakan gwamnononin Taraba, Filato, Adamawa, da ma Sanatoci da
mambobin majalisar wakilai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here