An Sake Kama Kwamandan Boko Haram a Gidan Shugaban Karamar Hukuma

0
1054

Imrana Mustapha, Daga Kaduna

 A kokarin da rundunar tsaron Najeriya ke yi domin ganin an kawo karshen matsalar tashin hanlalin Boko Haram a ranar Juma\’ar da ta gabata suka kama wani Kwamandan boko haram a cikin Gidan wani shugaban karamar hukuma a Borno.

Rundunar sojan Najeriya a karkashin Operation Lafiya Dole da ke aiki a Jihar Borno da wasu wurare na yankin Arewa maso Gabas suka samu nasarar kame wani daga cikin kwamandojin boko haram da ake nema ruwa a jallo.

Bayanan da aka samu sun tabbatar da cewa shi kansa shugaban karamar hukumar an kame shi kuma an kame shi ne saboda boye kwamandan na boko haram wanda ya zuwa yanzu ba a bayyana sunansa ba, an kuma kama shi ne a rukunin gidaje Dubu daya a kan titin Maiduguri zuwa Damaturu zuwa Kano

Rahotannin sun ce wani da yake zaune a rukunin gidajen ya ce kama shugaban karamar hukumar bai zo masu da makaki ba saboda da yawa mambobin boko haram da suka gudo daga Sambisa a nan suke zaune tsawon lokaci.

Rahotannin sun ci gaba da cewa karamar hukumar na da nisan kilomita 40 ne daga birnin Maiduguri babban birnin Jihar Borno.

An tabbatarwa majiyarmu cewa jami an tsaron sun isa gidan ne bayan da suka samu rahotanni cewa kwamandan yana cikin gidan.

Shugaban karamar hukumar da Kwamandan boko haram din suna hannun jami an tsaron soji domin binncike a kan lamarin.

Sai dai duk kokarin da aka yi na jin ta bakin jami\’an tsaron yan sanda bai samu nasara ba domin mai magana da yawun rundunar Victor Isuku, an kasa samunsa a waya.

\”An dai samu nasarar kame mutanen biyu ne a ranar Juma ar da ta gabata\”inii majiyarmu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here