BA RUWANMU DA RIKICIN KADUNA – INJI FULANI

0
1005

Usman Nasidi Daga Kaduna

KUNGIYAR Fulani ta musanta zarge-zargen da wasu ke yi cewa su ne ke kai hare-hare a kudancin jahar.
A wani taron manema labarai a Kaduna,al\’ummar Fulanin sun ce ba zaunannun Fulani na kudancin jihar ne ke kaddamar da hare hare ba, mai yiwuwa wasu Fulani ne dake zuwa yankin daga waje.
A halin yanzu dai an kafa dokar hana fita ta sa\’o\’i 24 a wasu kananan hukumomi na jihar sanadiyyar rikice-rikice tsakanin fulanin da wasu kabilu.
Rahotanni sun ce an yi asarar rayuka da dukiyoyi a hare hare na baya bayan nan da wasu \’yan bindiga suka kaddamar a Kudancin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here