Kwamishinan \’Yan Sanda Ya Kashe Kansa Da Bindiga

0
963

MUSA MUHD.KUTAMA, Daga Kalaba

MATAIMAKIN kwamishinan ‘yan sanda ya kashe kansa sakamakon bakin ciki da larurar da Allah ya jarrabe shi da ita ta shanyewar barayin jiki . ACP  Christopher Osakue,yadda wannan jarida ta samu labari ya kashe kansa ne a Benin babban birnin jihar Edo.

Kafin mutuwarsa Gaskiya Ta Fi Kwabo ta samu labari a da can  shi ne mai kula da shashen bayar da horo na rundunar ‘yan sanda da ke jihar Ondo yammacin kasar nan kafin daga bisani aka sauya masa wurinn aiki  aka dawo dashi jihar Edo domin ci gaba da wani aikin, daga bisani kuma  a gidansa da ke unguwar Upper Sokponba ya harbe kansa . Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan wanda ya yi fama da cutar shanyewar barin jiki an ce bindigarsa fistol ya dauko ya harbe kansa da ita .

Da yake tabbatar wa manema labarai afkuwar lamarin kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo  Haliru Gwandu, ya ce bindigar da Osakue, ya harbe kansa da ita wadda aka ba shi ce a lokacin da yake aiki a jihar Ondo kafin daga bisani kuma a dawo da shi Edo.Ya kuma bayyana mutuwar jami’in nasa da cewa kisan gilla ya yi wa kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here