Ungo-zoma Ta Cire Hannun Jariri Yayin Karbar Haihuwa

0
996

Musa Muhammad Kutama, Daga Fatakwal

GWAMNATIN jahar Legas ba tare da bata wani lokaci ba ta sa a  rufe wata cibiyar unguwar zoma mai zaman kanta  da ta ke karbar haihuwa mai suna Oyekanmi da ke yankin Odogunyan, Ikorodu birnin Legas sakamakon rahoton da ta samu na wata unguwar zoma[an sakaya sunanta]  mai kartbar haihuwa da ke zaman kanta ta cire hannun wani jariri yayin da take kokarin zakulo shi daga cikin mahaifiyar da nakuda ta zo mata da gardama.

Unguwar zomar wadda ke kokarin agaza wa mata mai nakkuda wadda take kokarin haihuwa, wajen ciro yaron daga mahaifa ne ta fisgo hannun jaririn wanda ya tsinke daga jikinta aka haifi yaron babu rai yayin da aka dauki matar mutu kwakwai rai kwakwai zuwa babban asibitin Ikorodu .

Nan take da gwamnati ta samu labarin abin da ya faru, sai mai ba Gwamna shawara ta musamman kan harkokin kiwon lafiya  Dokta Olufemi Onanuga ya bada umarni a rufe cibiyar karbar haihuwa ta Oyekanmi ba tare da jinkiri ba

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ta jihar Legas Adeola Salako,ya ce gwamnati ta sanya a yi binciken yadda ma aka yi har hakan ta faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here