Za Mu Magance Rikicin Kudancin Kaduna : Bukola Saraki

  0
  797

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  SHUGABAN majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, ya yi alkawarin za a gudanar da bincike kan rikicin da ya janyo salwantar rayuka da kadarori a kudancin jihar Kaduna.
  Mataimaki na musamman ga kakakin majalisar Bamikole Omishore, ne bayyana haka, a matsayin maida martani ga wani dan Najeriya da ya gabatar da koken hakan ga minista a shafinsa na Twitter.
  Wani dan Najeriya Chimeze Okoro Ukoha, ne ya wallafa koken a shafin sa na Twitter, inda ya ce an kashe mutane sama da 800 kudancin Kaduna amma babu wanda ya ce uffan kan batun.
  Saraki ya bashi amsar cewa da zaran majalisar ta dawo aiki za ta yi bincike kan lamarin domin gano asalin abin da ya faru da kuma magance matsalar.
  Ya kara da cewar rayuwar kowanne dan Najeriya na da muhimmanci, kuma majalisar za ta tabbatar da cewar an bi doka kammar yadda tsarin mulki ya tanada.
  Ya ce za kuma a yi hakan ne ta hanyar tuntubar \’yan majalisar da suka fito daga yankin dan gano bakin zaren.
  Kashe-kashen kudancin Kaduna na cigaba da jefa jama\’a mussamman ma talakawa cikin mawuyacin hali.
  Wasu \’yan Najeriya dai sun kasa gane dalilin kasa shawo kan matsalar, duk da cewa gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta wadata yankin da jami\’an tsaro

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here