Ta Gutsure Kunnen Matar saurayinta

0
1102

Musa Muhammad kutama Daga Kalaba

KISHI kumallon mata ,yan sanda a kasar Kenya sun cafke wata mata mai suna Bor saboda samunta da laifin cije kunnen matar saurayinta mai suna Grace Washeko, ta kuma hadiye guntun  kunnen da ta ciza .Wannan lamari ya faru ne tsakanin Bor da Washeko wata cacar baki ce mai zafi aka ce ta hada su daga nan fada ya kaure sai Bor ta yi sa’ar cika bakinta da kunnen Grace ta gutsurer mata shi ta kuma ta hadiye kamar yadda aka ruwaito.

Washeko,Yanzu haka tana kwance a wani asibiti. Tun farko kamar abin arziki Bor ta kai ziyara gidan su Grace Washeko da nufin ganin dan abokin aiknta abu kamar wasa sai ta fara tsokanar Grace daga nan fada ya rikice tsakanin su.Wannan lamari ya yi matukar ba mutanen wannan yanki na Voi mamaki .

Daga bisani babban jami,in‘yan sanda da ke Kandera OCPD,Gregory Mutiso ya ce va binciken da sukam fara yi iyayen mijin sun gargade shi da ya daina soyayya da matar lamarin da ya kekasa kasa ya ki ji .Bincike na nan ‘yan snada na yi kan lamarin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here