Waka Hanya Ce Da Ke Kara Hada Kan Al\’umma – Bida

0
1142

Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba

AN bayyana waka a matsayin wata hanya da ta ke kara hada kan jama’a ba tare da nuna banbancin harshe ko kabila kana kuma tana kara habaka dankon al’adu.

Alhaji Hamza Bida wani shahararren mawaki a kasar Bidda jihar Neja ne ya fadi haka yayin wata ziyarar aiki da ta kawo shi Kalaba suka zanta da wakilinmu na kudanci.

Ya ce shi wakokinsa duk da ya saba yana yin su baya yin wakar da za ta zama cin fuska ga wata kabila ko wani addini a’a wakoki ne yake yi na hada kan jama’a da ‘yan kasa baki daya.Bayan harshen Nupe mawakin yana iya yin waka ma da harshen Ingilishi da kuma Ibo musamman irin yadda ya yi wa Gwamnan Kuros Riba Sanata Farfesa Ben.Ayade waka cikin harshen Turanci dana Ibo “ai saboda jin dadin wakar ce ma ya yi mini sha tara ta arziki na yi ta ne da harshen Ingilishi da na Ibo, tsammanina yana jin harshen Ibo”inji shi.

Ya ci gaba da cewa wakokinsa duka na hadin kan kasa ya fi yawan yi sannan kuma yana ma yi wa sarakuna da masu mulki a cewarsa fatansa ya ga an zauna lafiya ba tare da nuna wa juna wani banabncin kabila ko harshe ba ko na addini “tun da har ga shi na zo kudanci na ga ‘yan uwana ‘yan arewa suna zaune lafiya da ‘yan asalin jiha ka ga zan je in karas da cewa na ga ‘yan uwana yan arewa kamar ma ni ma ina arewar abin gwanin ban sha’awa .inji Hamza.

Karshe ya nuna matukar gamsuwa da zuwansa Kalaba ya ga dangi da ‘yan uwa kamar yana gida. Ya yi fatar alheri tare da dorewar zaman lafiya ko ina a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here