Hadaddiyar Kungiyar Izala Na Da Wa\’azin Kasa Gobe Da Jibi A Kaduna

0
2736

Zubair Abdullahi Sada, Daga Kaduna

HADADDIYAR kungiyar nan ta addinin Musulunci, Jama\’atu Izalatil Bid\’a Wa Ikamatis Sunnah na da gagarumin wa\’azin kasa da ta shirya gudanarwa a garin Kaduna garin Gwamna a karkashin jagorancin shugaban majalisar malamai na kasa, As-Sheik Muhammad Sani Yahya Jingir da mataimakinsa na I As-Sheikh Yusuf Muhammad Sambo da mataimakinsa na II, As-Sheikh Sa\’eed Al-Hassan Jingir.

Wakilin Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ya ruwaito cewa, Babban jami\’in hulda da jama\’a na kungiyar, Honorabul Ashiru Muhammad ne ya bayyana haka ga manema labarai cikinsu har da wakilin namu.

Ya ce wa\’azin kungiyar ba wani boyayyen abu ba ne, ko kuma sabon abu, domin kungiyar ta Izala Kaduna gidanta ne na farko na akida idan uban kungiyar As-Sheikh Abubakar Mahmud Gumi Allah Ya gafarta masa ya fareta ta hanyar koyarwarsa da bin Sunnar Manzon tsira Muhammad SAW inda ya bai wa jagoran kungiyar As-Sheikh Isma\’il Idris Jos (Allah Ya gafarta masa) kwarin gwiwa matuka, aka ci gaba da yada Kitab littafi Alla SWT da Sunnar Manzon Allah SAW.

Malamai da dama za su gabatar da wa\’azi na dare a ranar Asabar da kuma safiyar Lahadi in sha Allahu. Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo za ta kawo maku bayyanan wa\’azin kai tsaye daga munbarin wa\’azin a rubuce in Allah Ya yarda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here