FIFA Ta Hana NFF Dala Miliyan 1.5 Dalilin Birbishin Cin Hanci A Hukumar

  0
  829

  Musa Muhammad Kutama Daga Kalaba

  HUKUMAR kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta yanke shawarar hana wa hukumar kwallon kafa ta Nijeriya NFF tallafin Dala Milyan daya da rabi [$1.5] kamar yadda ta saba ba kasashe don su bunkasa harkokin wasanni a kasashen su dalili  saboda zarginta  gano birbishin cin hanci da rashawa a hukumar game da yadda ta kashe kudaden da aka riga aka ba ta lokacin baya.

  Gaskiya tafi kwabo ta ruwaito hukumar da ke kula da harkokin kwallon kafa a nahiyar afrika wato African Football ta hakaito FIFA tab a hukumar NFF ta nijeriya takardar gargadi na karshe ga hukumar kwallon kafar nijeriya saboda rashin gamsuwa da yadda tayi da tallafin baya da hukumar kwallon kafa da duniya ta bata.

  Masoya kwallon kafa a nijeriya sun nuna takaicin su bisa yadda a Nijeriya hukumar kwallon kafar kasar ke yin yadda taso kama tun daga alwu-alawus da hakkokin ‘yan wasa akasarin wadanda suka tofa albbarkacin bakin su da wakilinmu na kudanci ya zanta dasu sun nuna matukar idan ba,a tashi tsaye ba wannan halin an iya nakasa harkokin wasannnin motsa jiki a kasar nan .Idan za,a ya tunaw ama kwanan baya said a tsohon mai horas da kungiyar wasan kwallon kafar kasar wato super eagles, Adoboye Onigbinde ya yi hasashen idan ba,a dauki kwakkwaran mataki ban an da shekara hudu masu zuwa harkar kwallon kafar Nijeriya ka iya zama sai tarihi.

  Wannan gargadi na jan kunne da FIFA tayi wa hukumar na tasan yadda take batar da kudinta ne kuma ta shiga taitayinta.Tuni aka ruwaito ministan harkokin matasa da wasanni Barista Solomon Dallung ya nuna fushins agame da irin wadan nan halaye da hukumar kwallon kafa ta Nijeriya take nunawa.

  Kungiyoyin da ke karkashin hukumar wasan kwallon kafa ta duniya karkashin jagorancin shugabanta Giani Infantino na karbar tallafi daga hukumar kowace shekara ana ba hukumar at nijeriya dala 250,000 kafin daga bisani hukumar fifa ta kara kudin yawan su ya koma dala milyan daya da rabi.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here