Rahama Sadau Ta Karyata Batun Da Ake Yadawa Na Ta Yi Ridda

0
1423

Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba

FITACCIYAR jarumar fina-finan Hausa da aka kora daga harkar yin fim a Nijeriya, Rahama Sadau ta fito fili ta karyata rade-radin da ake bazawa a kafafen sada zumunta cewa korar da akayi mata daga harkar fina-finan hausa ta yi kaura ta koma kasar Amurka kuma wai za ta yi ridda ta koma kirista .

Sadau dai wadda ta shafe watanni a kasar ta Amurka sakamakon amsa goron gayyata da wani shahararren mawaki mai suna Akon ya yi mata tun komawarta can aka yi ta yamadidi da kuma baza jita-jita wai za ta yi ridda  lamarin da ita kuma ta fito fili ta karyata ta ce ba gaskiya ba ne.

Ta ce “karya ce tsagwaronta ake shara mini, wannan jita-jita ban ji dadin ta ba ga shi har hakan ya sanya malaman addini iyaye da sauran manya suna ta nuna mini bacin ransu a kan zargin da ba su bincika ba kuma babu kamshin gaskiya cikinsa”

Ta ci gaba da cewa sana’ata da na kwarai a kai babu kasar da ba za ta iya kai ni ba in yi ta kuma imanina yana nan daram ba zai taba canzawa ba, ba kuma zan canja ba”inji Rahama Sadau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here