Rahama Sadau Ta Ragargaji Filin Jirgin Sama Na Kaduna

0
1047

Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba

KORARRIYAR jarumar fina-finan Hausa Rahama sadau ta ragargaji filin jirgin sama na Kaduna ta ce babu lallatattcen filin jirgin sama a Nijeriya kamarsa.Sadau wadda ta fadi a sakon da ta aike ta shafinta na twitter gaskiya ta fi kwabo ta yi tozali da shi ta yi rubutun kamar haka”babu talautaccen  filin jirgin sama kamar na Kaduna” .

Ta ci gaba da rubuta “kowa ka gani daga cikin maaikatan filin jirgin yan Allah ba ni in batar ne kamar kai ka hana masu albashi “injita .

Jarumar wadda yanzu haka ke gudun hijira kasar Amurka a rubutunta na shafin twitter ta kara da cewa “kowa ka gani daga cikin su babu maid a,a”.

Wakilinmu na kudanci ya yi bakin kokarinsa domin jin martanin mahukuntan filin jirgin saman na Kaduna amma abin ya faskara

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here