NFF Za Ta Duba Filayen Inugu, Bauci Da Fatakwal Don Buga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika

  0
  370

  Musa Muhammad Kutama,Daga Kalaba

  HUKUMAR kwallon kafa ta Nijeriya wato NF ta ayyana aniyarta na zagaya wasu daga cikin filayen wasanni hudu da za,yi gasar cin kofin zakarun Nahiyar Afrika da suka hada da Bauci,Inugu da  Nnewi, da kuma Fatakwal da aka ware domin yin wasannin su na  gida a filayen wasannin kungiyoyin da za su wakilci Nijeriya a gasar cin kofin zakarun Nahiyar.

  Kamar yadda gaskiya ta fi kwabo ta samu jadawalin, sun hada da kungiyoyin Enugu Rangers, zakarun kofin Premier na Nijeriya da kuma kungiyar Ribas United. Sauran su ne Ifeanyi Ubah na garin Nnewi, da su ma suka lashe kofin charity bayan lallasa zakarar Nijeriya ta Premier Enugu Rangers da ci 4 da 3 sannan kuma kungiyar Wikki Tourist ta Bauchi .

  Hukumar ta ce ta yanke shawarar hakan ne a ganawar da ta yi da masu ruwa da tsaki na kungiyoyin da kuma mambobin hukumar a Abuja kwanan baya .Da yake sanar da haka ga manema labarai Daraktan shirya gasar Bola Oyeyode ya ce “duk ilahirin filayen  wasannin da kungiyoyin da za su yi wasannin su na  gida wakilan hukumar kwallon kafa za su duba su domin  su ga cancantar su ko akasi kafin a fara gasar da kungiyoyin za su wakilci Afrikan za su  fara”inji shi.

  Daraktan shirya gasar Oyeyode, ya kara da cewa daga cikin abubuwan da za a duba sun hada da “kula da lafiya, tsaro da kuma kayan kula da lafiyar ‘yan wasa”.saboda mahimmancin da suke da shi kungiyar Enugu Rangers ce da takwarrata ta Ribas United za su wakilci Nijeriya a gasar yayin da su kuma kungiyoyin Ifeanyi Ubah da Wikki tourist za su fafata a gasar kofin kalubale

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here