ANA ZARGIN WASU \’YAN SANDAN JIHAR KANO DA YI WA WANI MUTUM KISAN GILLA

0
854

Daga Usman Nasidi

MAJALISAR wakilan Najeriya ta umarci kwamitin ta mai bin diddigin korafin jama’a, ya gudanar da bincike dangane da zargin da ake yi wa ‘yan Sanda a Kano na kisan gilla ga wani mutum mai suna Ibrahim Badamasi na kauyen Gundutse da ke yankin karamar hukumar Kura.
Al’amarin dai ya faru ne a ranar 14 ga watan Nuwambar bara a yayin arangama tsakanin ‘yan shi’a da ‘yan sanda akan hanyar Kano zuwa Zariya.
Wasu gungun Lauyoyin kare hakkin bil- Adama ne suka rubuta takardar korafin ga majalisar wakilan ta Najeriya, suna neman a dauki matakin da ya kamata a kan ‘yan sanda, da kuma jami’an kiwon lafiyan da ake zargi da hannu wajan mutuwar wanna magidanci da ya mutu ya bar ‘ya’ya bakwai da mata biyu.
Garba Ibrahim Diso, dan majalisar, da ya karata takardar korafin ya ce lauyoyi ne suka rubuto zuwa ga kakakin majalisar tarayya kuma kakakin ya tura ga kwamitin da ke kula da korafe korafe.
Baya ga neman diyyar fiye da Naira miliyan saba’in da biyu, lauyoyin na bukatar a hukunta duk masu ruwa a cikin wannan al’amari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here