Manoma ne kan Gaba Wajen biyan Kudaden Aikin Hajji A jihar Kaduna

0
1182

Isah Ahmed Daga  Jos

BISA ga dukkan alamu manoma ne kan gaba wajen biyan kudaden kujerun aikin
hajjin bana a jihar Kaduna, da aka fara makonni biyu da suka gabata.
Binciken da wakilinmu ya gudanar a wasu kananan hukumomin jihar,
dangane da yadda maniyyatan  suka fara biyan kudaden kujerun aikin
hajjin  baya.  Ya gano cewa a yankunan kananan hukumomin da manoma
suke a jihar, kamar Lere da Kubau da Soba da Giwa da Makarfi da Ikara
alhazan suna ta zuwa suna biyan  kudaden kujerun aikin hajjin, tun
daga naira miliyan 1 da dubu 200 zuwa naira miliyan 1 zuwa naira dubu
800.
Amma a binciken da wakilinmu ya gudanar  a kananan  hukumomin Kaduna
ta arewa da Kaduna ta kudu ya gano cewa  ga jami\’an hukumar jin dadin
alhazai nan da aka tura, don yi wa maniyayyata  rigista  suna jira amma
babu alhazan.
A zantawarsa da wakilinmu wani manomi daga karamar hukumar Lere da ya
biya kudin kujerar aikin hajjin bana, mai suna Ibrahim Muhammad Sani
ya bayyana cewa abin da ya karfafa masa gwiwar biyan kudin kujerar
aikin hajji a bana, shi ne farfadowar aikin noma.
Ya ce a shekarun baya manoma  suna noman ne amma babu riba sai faduwa,
amma a wannan shekara Allah ya kawo darajar amfanin gona.
\’\’Na sami amfanin gona mai yawa a daminar bana, kuma Allah ya kawo
darajarsa na samu na biya wannan kudin kujerar  ba tare da wata matsala
ba, kuma na sayi takin da zan yi noma a damina mai zuwa\’\’.
Shi ma a zantawarsa da wakilinmu wani manomi daga jihar  mai suna
Sunusi Bala ya bayyana cewa noma ne ya karfafa masa gwiwar biyan kudin
aikin hajjin bana.
Ya ce a da mu manoma mai sayen amfanin gona ya sayar, ya fi mu cin riba,
mu  mun zama kamar bayi. Amma sakamakon canjin gwamnati da Allah ya
kawo mana amfanin gona ya yi daraja.
\’\’A bana \’yan buhuna kadan na fitar na sayar na biya wadannan kudade
har naira miliyan 1 na kujerar aikin hajjin bana. Kuma na riga na sayi
takin zamani da kashin kajin da zan yi noman damina mai zuwa\’\’.
Jami\’in hulda da jama\’a na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna
Alhaji Yunusa Muhammed Abdullahi  Makarfi wanda aka tura karamar
hukumar Lere, don kula da yi wa maniyatan rajista ya tabbatar da wannan labari.
Ya ce ko a nan cibiyar rajistar alhazai ta karamar hukumar Lere,
alhazai da dama sun fito domin biyan kudaden kujerar aikin hajjin
bana, kuma mafiya yawan alhazan manoma ne.
Ya ce a bana hukumar alhazan ta yi kyakkyawan tsari wajen ganin alhazai
sun biya kudaden kujerun aikin hajjin bana, ba tare da sun fuskanci
wata matsala ba.
Ya yi kira ga maniyyatan  su rika yin hulda da jami\’an hukumar alhazai
kai tsaye, su guji  bi ta hanun wasu mutane wadanda ba ma\’aikatan
hukumar alhazan ba ne.
Ya ce a bana duk wuraren da ake biyan kudaden alhazai a jihar Kaduna,
maniyyaci ya riko fasfo dinsa ya zo nan take, za a yi masa rajista a
ba shi takarda ya je banki ya biya kudin kujerarsa ba tare da wata
matsala.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here