Ba A Bar Guragu Baya Ba A Garin Kalaba – Muhammad Buhari

0
1135

MUSA MUHD.KUTAMA,  Daga  Kalaba

GURAGU ‘yan asalin Arewacin Nijeriya mazauna garin Kalaba Jihar Kuros Riba sun kafa kungiya mai suna kungiyar nakasassu guragu mazauna Kalaba watanni biyar kenan   .Sakataren kungiyar Muhammadu Buhari Isah ne ya shaida wa wakilinmu na kudanci haka yayin tattaunawarsu da shi.

Ya ce sun yanke shawara su  kafa kungiyar ce domin  shi ne “ mu guragu wadanda muke nan garin Kalaba mun kafata ne domin mu kawo ci gaban rayuwar mu”.Da yake yin karin haske game da makasudin kafa kungiyar wadda ita ce ta farko a tarihin zama da zuwan guragu harkokin nema Kalaba sakataren ya ce “wanna kungiya mun kafata ne saboda  irin al’amuran da suke tafiya na yau da gobe , a rayuwa ana so idan kuka zo kuka zauna a wuri  ya kasance kuna da shugaba saboda duk wani abu na ci gaba da zai taso idan kuna da shugaba ,idan koda gwamnati ta tambayeku ko wani ya ce ina shugabanku kuka nuna to zai dauke ku da muhimmanci  saboda haka ne ya sa domin mu kare mutuncin kan mu ne a idon al’umma”.

Da aka tambaye shi ko tilas ce ta sanya su kafa kungiya, Buhari Isah sakataren kungiyar guragu ya ce, ‘’a,a ba uwar bari muka gani ba mun yi haka ne domin mu jawo hankalin ‘yan uwanmu  ,mu nuna masu zaman kara-zube akwai matsala,  shi ya sanya muka jawo su jiki domin mu nuna masu muhimmancin ci gaban rawuyarmu idan muka kafa kungiyar “.Ya ci gaba da cewa daga dan abin da Allah ya huwace masu ne ko wane mako idan sun zauna  zaman tattaunawa suke ajiye dan wani abu saboda koda wata larura ta jinya ko  hadari ko kuma wani abu daban ya samu daya daga cikinsu ba  sai sun tsaya suna nema a  gurun jama’a ba, domin ai yau da gobe sai Allah.

Karshe ya yi bayanin dangantaka tsakaninsu da ‘yan uwa ‘yan  arewa da kuma ‘yan asalin Kuros Riba ya ce wannan babu wata matsala tsakaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here