AN KASHE WANI DAN SANDA A JIHAR FILATO

0
1013

Daga Usman Nasidi

WASU ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari wani ofishin ‘yan sanda a Dengi a karamar hukumar Kanam ta Jihar Filato.
A cewar rahotanni, ‘yan bindigan sun yi nasarar hallaka wani dan sanda sannan kuma su ka yi awon gaba da bindigogi.
Harin da ‘yan bindigan su ka kai ya faru ne a daren Lahadi 23 ga watan Janairu a inda suka hallaka wani jami’in ‘yan sanda suka kuma jikkata wasu da dama.
Wata majiyar ‘yan sanda a ranar Litinin 23 ga watan Janairu ta ce, kwamishinan ‘yan sandan jihar Peter Ogunyanwo ya kai ziyara inda aka harin domin gane wa idonsa barnar da aka yi.
Kauyen Dengi mai kimanin nisan kilomita 150 daga Jos babbar birnin jihar, na  tsakiyar jihar ne.
Irin wannan dai ta faru kimanin watanni uku da suka wuce a kauyen Igumale a karamar hukumar Ado ta Jihar Binuwai,
wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wani ofishin ‘yan sanda, a inda suka hallaka wasu jami’an ‘yan sanda uku, tare da jikkata wani, bayan da suka kwashe bindigogin da ke ofishin a watan Oktobar shekarar 2016 ta wuce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here