MATAKAN DA EL-RUFA\’I YA DAUKA DON MAGANCE RIKICIN KADUNA

0
848

Daga Usman Nasidi

-GWAMNAN Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kayyade matakai Uku da Gwamnatinsa ke dauka domin kawo karshen rikici da kashe kashen da ya ki ci ya ki cinyewa a kudancin jihar.
A jawabinsa yayin da ya karbi bakuncin majalisar sarakunan jihar a karkashin jagorancin Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.
Gwamnan ya bayyana cewa mataki na farko da ya dauka shi ne na ganawa da shugaban hafsan soji domin neman a girke bataliyar sojoji biyu a yankin, daya a Kachiya daya kuma a Kafanchan.
Ya ce za a gina wa sojojin bariki a yankunan da za su zauna domin tabbatar da tsaro, Sauran matakan sun hada da kamo wadanda suke da hannu a tada rikicin da kashe kashen sannan a gurfanar da su a gaban shari\’a domin hukunta su.
Sai kuma batun zaman sulhu da duka bangaririn, kuma tuni ya gayyaci cibiyar wanzar da zaman lafiya da ta jagoranci sulhunta rikicin jihar Plateau da su zo kudancin Kaduna su shiga tsakani a tattauna da duka bangarori domin nemo mafita ta karshe a kai.
El-Rufai ya kuma sake jaddada cewa shi da mataimakinsa da sauran mukarrabansa sun rantse da Alkur\’ani da Bibul gabanin fara aiki da nufin za su yi aiki tsakaninsu da Ubangiji ba tare da nuna fifiko ko son kai ba, yana mai cewa akan haka suke jagorantar jihar tsakani da Allah ba tare da nuna fifiko a kan kowane bangare ko nuna wariya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here