Alhinin Rasuwar Baba Masaba, Mai Mata 86

0
1051

Rabo Haladu Daga Kaduna

BABA Masaba, wanda dan asalin garin Bidda ne da ke jihar Neja  ya mutu ne a ranar Asabar.
Rahotanni sun ce ya mutu ne yana da shekara 93.
Baba Masaba dai ya yi fice ne saboda yawan mata da \’ya\’yansa.
Shi dai marigayin – wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya – ya fito fili ne bayan da a wata hira ta musamman da ya yi da manema labarai  ya ce ya auri mata 86 kuma dukkansu suna tare da shi a lokacin, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce tsakaninsa da Malaman addinin Musulunci.
Bayanai sun nuna cewa Baba Masaba yana biya wa dukkan iyalinsa bukatunsu duk kuwa da yawansu.
A wani lokaci can baya ma jami\’an tsaro sun taba tsare shi a birnin Mina na jihar saboda auren mata da yawa din da ya yi, abin da ya saba wa addinsa na Musulinci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here