Ya Karyata Jita-jitar Marinsa Da Ake Ta Yayatawa

  0
  890

  MUSA MUHD.KUTAMA, Daga Uyo

  MAI horas da kungiyar wasan kwallon kafa ta Akwa United da ke Uyo, jihar Akwa Ibom Abdu Maikaba ya karyata zargin da ake yadawa cewa  wani magoyin bayan kungiyar da ya  fusata ya kwada masa mari bayan an tashi wasa a fafatawar da kungiyar ta yi da takwararrta ta Enugu Rangers a filin wasa na Uyo, da suka tashi canjaras  .

  Maikaba ya karyata zargin jita-jitar da ake ta bazawa ta cika garin Uyo da cewa wani maigoyin bayan kungiyar Akwa United baya ya shara wa Abdu Maikaba mari ya ce “wannan ba gaskiya ba ne babu wani magoyin bayan kungiyar nan da ya mare ni”inji shi.

  Ya ce na ji mamaki da na karanta labarin da aka wallafa a intanet,  daya daga cikin jaridun da ake wallafawa sun bada labari wai wani magoyin bayan kungiyata ya mare ni, wannan sam-sam ba haka ba ne karya ce tsagwaronta”inji Maikaba.

  Maikaba dai tsohon mai horas da kungiyar wasan kwallon kafa ta Wiki Tourists da ke garin Bauchi ce kafin daga bisani su raba gari da kungiyar ya dawo Akwa United.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here