An Damke Masu Yi Wa Mata ‘Yan NYSC Fyade

0
1259

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

RUNDUNAR ‘yan sandan Jihar Abiya ta sanar ka kama wasu mutane hudu da suka addabi mata masu aikin yi wa kasa hidima a jihar fyade. Sashen kula da masu aikata miyagun dabi’u da kuma yaki da ta’addanci na rundunar ‘yan sandan jihar ne ya sanar da haka ga manema labarai.

Wadannan takadarai da suka hana mata sakat da yi masu fyade, sata da kuma tare su a hanya ko kudi ko ko fyade dai suna bin kasuwannin kauyuka ne suna tare matan da suka ayyana yi wa satar ko kuma fyade a kan hanyar  kasuwar kauyen Elughu, da ke karamar hukumar Ohafia.sun shiga hannun jami’an ne bayan wata da aka yi wa fyade ta kai karar su wajen ‘yan sanda.

Mutanen hudu da aka kama ake zargi su ne Nkeiru John Iwuoha, da  Ifeagwu Kalu, sauran su ne  Chukwu Ogbonnaya, da  Onyebuchi Kalu.Da yake gabatar da su gaban manema labarai kwamishinan ‘yan sandan jihar Abiya   Adeleye Oyebade, ya ce “mata ‘yan kasuwa masu shagunan a kasuwar ne suka yi kwarya-kwaryar yajin rufe shagunan su domin nuna takaicin su game da wannan mummunar dabi’a ta fyade da ake yawaita yi a kasuwar ko kuma mata abokan huladar su ta cinikayya ake wa fyade idan sun bar kasuwar hanyar su ta koma gida ana masu kwantan bauna”.inji shi.

Daga nan   kwamishinan ya bai wa al’ummar jihar tabbacin su kwantar da hankalin su, rundunar sa za ta yi bakin kokari ta ga ta murkushe duk wani tsagera mara da’a a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here