MAWAKI TUFACE YA SOKE ZANGA-ZANGAR DA YA SHIRYA GUDANARWA

0
760

Daga Usman Nasidi

MAWAKI Tuface ya soke zanga-zangar kin jinin gwamnati da ya shirya yi a Legas da kuma Abuja a ranar Litinin 6 ga watan Fabarairu.
Mawakin ya bayar da sanarwar soke zanga-zangar ne a shafinsa na dandalin sada zumunta na Instagram a ranar Asabar 4 ga watan Fabarairun shekarar 2017.
Mawakin ya bada matsalar tsaro a matsayin dalilin soke zanga-zangar yana mai cewa, zanga-zangar na fuskantar mummunan barazanar kutse daga wasu bata-gari.
A baya dai Tuface ya dage sai an yi zanga- zanga har ma ya bayar da samfurin irin launin shigar da za a yi domin maci na lumana a wuraren zanga-zangar.
Zangar da aka shirya ta ja hankalin \’yan Najeriya a lokacin da shahararren mawakin ya hada gwiwa da \’yan kungiyar Tura ta kai Bango watau \’Enough is Enough\’ da ta shirya zanga-zangar.
Kuma da yawa daga shahararrun mutane makada da \’yan wasan kwaikwayo da makamantansu suka yi alkawarin bayyana a wuraren da za a yi.
To amma akwai shiri daga \’yan sanda na hana gudanar da zanga-zangar ta lumana a kan gwamnatin da shugaba Buhari ke jagoranta.
To sai dai kuma an samu yarjejeniya ta fahimtar juna inda \’yan sandan yanzu za su bada tsaro ga mutane.
Tuface wanda ake wa kallon wanda ya dauki gabarar gudanar da zanga-zangar ya wallafa wani hoto a shafinsa na Instagram inda ya bukaci \’yan Najeriya su yi fitar dango a sassan kasar nan daban-daban.
Wadanda ke Legas za su hadu a filin wasan kwallon kafa na kasa da misalin karfe 8 na safe, yayin da wadanda ke Abuja za su hadu a Unity Fountain da misalin karfe 9 na safe.
Ya kuma bukaci \’yan Najeriya su sanya korayen kaya yayin da zu nuna bukatunsu ga gwamnatin tarayya lokacin da talakawa ke cikin ukuba da rashin ababan more rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here