Rana Ta Baci Wa Barauniyar Jariri A Ikko

0
1108

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga, Kalaba

SACE jariri dan wata biyu da haihuwa a kasuwar Badagry da ke birnin Legas ya jefa iyaye da ‘yan kasuwar cikin mummunan firgici. Jaririn  kamar yadda wannan jarida ta samu labari mai suna  Kudus Adebowale, an ce uwarsa Alimat Adebowale , tana bakin shagonta da take gudanar da kasuwanci tana tsakar ciniki dama kuma babu abin da take sayarwa face biskit, kwastomomi sun cika mata shago sai wata yarinya da ake wa lakabi da T-girl ta shigo shagon ta ce mata ta ba ta jaririyar ta rike mata, da farko sai matar ta ki ita kuma yarinyar da mayatar sai an ba ta har ma aka ce ta tambayi uwar ko sun taba samun wani sabani ne da ba za ta barta ta dauki ‘yar ba ganin kowa yana zuwa yana daukar jaririn ana ta taya ta murna sai uwar ta bata jariryar ta dauka.

Majiyarmu ta ci gaba da cewa T-girl da naci sai da ta zauna uwar yaron ta shayar da shi da ta gama ta ba ta ta dauka ta goya yaro a bayanta ta tafi kamar za ta rika yin wasa da sauran yaran da iyayensu suka zo da su kasuwa tana goye da shi bayan da hankali ya kwanta Madam Alimat  ta gama sallamar abokan hulda shiru-shiru ba T-girl ba yaro Kudus daga nan ne fa aka fara cigiya ko ina yarinya ta shiga da goyon dan mutane daga nan ba,,a yi jinkiri ba aka sanar wa ofishin ‘yan sanda na Badagry .

‘Yan sanda suka baza komarsu suka sanar da duk wasu jami’ansu da ke a kan manyan hanyoyi suna aiki ga abin da ya faru ana cikin haka can a hanyar Ibadan ashe can T-girl da ta sulalle daga Badagry ta shiga mota ta tafi aka yi sa’a mota sai ta samu matsala direba kuma ya ce wa fasinjansa su yi hakuri ya gyara daga bisani yaro Kudus fa sai ya fara kuka yana son shan mama fasinjoji da ke cikin motar suka ce mata ta sauke yaron ta ba shi nono daga nan  barauniyar yaro ta daburce, ta haka aka  gano cewa ga alama ba danta ba ne daga nan aka jawo hankalin ‘yan sanda suka zo aka tafi da ita.

Daga bisani  Taofiq Adebayo jami’in kungiyar masu sufuri ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce an mika ta ofishin ‘yan sanda da ke Badagry, su kuma daga bisani sun kaita kotu.wadda ake zargin kamar yadda rundunar yan sanda ta tabbatar wa manema labarai da aka kamata ta ce “tsautsayi ne sharrin shaidan ne”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here