Makarantar Koyar Da Ilmin Kwanfuta Ta Green Heart Saminaka Tayi Bikin Yaye Dalibanta

0
1268
Isah  Ahmed Daga  Jos

MAKARANTAR koyar da ilmin kwanfuta ta Kungiyar Green Heart Impact Foundation da ke garin Saminaka a karamar hukumar Lere da ke jihar Kaduna tayi bikin yaye dalibanta karo na hudu.
Da yake jawabi a wajen bikin Mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani ya yabawa shugabar kungiyar Green Heart Impact Hajiya Munira Sule Tanimu saboda gina wannan makaranta  ta koyar da ilmin kwanfuta, a wannan yanki.
Ya ce  babu shakka wannan makaranta zata kawowa wannan yanki cigaba da daukaka, domin yanzu a duk duniya ana alfahari da ilmin kwanfuta. Ya yi fatar sauran masu hali da masu  ilmi  yankin  zasu yi koyi da wannan mata.
Sarkin wanda Wazirin Saminaka Alhaji Muhammad Rabi\’u Umar ya wakilta ya yi kira ga daliban da aka yaye suyi amfani da abubuwan da aka koyar da su a wannan makaranta, domin su taimaki kansu da kansu  da al\’ummar wannan yanki da qasa gabaki daya.
Shi ma a nasa jawabin wani malami a kwalegin ilmi ta jihar Kaduna da ke Gidan waya Kafanchan Malam Aminu Ahmed ya bayyana cewa yanzu ana wani zamani ne na amfani da na\’urar kwanfuta, a kowace irin rayuwa ta duniya.
Ya ce  nan gaba duk abin da mutum zai yi, idan bashi da ilmin kwanfuta abin ba zai yuwu ba. Don haka ya ce wadda ta gina wannan makaranta ta yi tunani kuma ta taimakawa al\’ummar wannan yanki. Ya yi kira ga masu hali da sauran al\’ummar  yankin,  su taimakawa  makarantar.
Daga nan ya yi  kira ga daliban da aka yaye  zasu yi aiki da ilmin da suka samu a  makarantar. Kuma  su bada gudunmawarsu wajen taimaka wa jama\’ar wannan  yanki.
Tun da farko a nata jawabin Ko\’odinatan wannan makaranta Safiya Tanimu Galma ta bayyana cewa sun shirya wannan taro ne don bikin yaye dalibansu karo na hudu. Ta ce a wannan karo sun yaye dalibai guda 50.
Ta ce an kafa wannan makaranta ne a shekara ta 2015 da manufar taimaka wa \’yayan talakawan wannan yanki su koyi ilmin kwanfuta kyauta.
Ta ce daga lokacin da aka kafa wannan makaranta zuwa yanzu sun yaye dalibai guda 200.
Safiya Tanimu Galma tayi bayanin cewa baya ga wannan makaranta, wannan kungiya ta Green Heart Impact Foundation tana da wasu makarantun  a Kano da Abuja da Kaduna da suke koyar da karatun kwanfuta kyauta.
Ta ce bayan haka  wannan kungiya tana tallafawa marasa lafiya da suke kwance a asibitoci da ziyartar gidajen yari don tallafawa fursunoni da dai sauran ayyuka na tallafawa al\’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here