Ya Kashe Mahaifiyarsa Don Ta Hana Shi Kudi

0
1055

MUSA MUHD.KUTAMA, Daga Kalaba

ANA zargin wani dattijo dan shekara 51 da  haihuwa a birnin Legas  mai suna  Oluwaseye Ayoola, da kashe mahaifiyarsa  mai suna Dorcas Ayoola, mai kimanin shekaru 81 ita ma da haihuwa  har lahira bayan da ya san ya aikata danyen aikin ya ranta-a-na-kare.

Da yake yi wa manema labarai Karin haske game da yadda ma aka yi har wanda ake zargin bayan ya aikata lafini ya gudu har kuma ma ya shigo hannu mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Legas SP Dolapo Badmos ya ce “bayan da muka samu shi ne bayan Ayoola ya aikata kisan sai ya sulale ya gudu da aka kawo mana rahoto shi ne muka baza komarmu kuma ta yi katarin kama shi .

Ya ci gaba da cewa wani dan uwansa ne mai suna  Akintunde Ayoola ya zo ya sanar da rundunar mu ya sanar da mu ko da muka je gidan muka tarar da gawar mahaifiyar tasu kwance cikin jini ta riga ta mutu shi kuma ba a iske shi a gidan ba ya riga ya tsere.

A bayanan da ya yi mana inji kakakin ‘yan sandan wanda ba tilas ta masa aka yi ba ya yi mana inji shi “ya je ne ya tambayi mahaifiyarsa ta ba shi kudi Naira Dubu goma sha daya don ta ki ta ba shi ne ya fusata ya fadata da duka .Yanzu haka wanda ake zargin na hannunj ‘yan sandan tsare idan an gama bincikensa kotu za a mika shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here