AKALLA SAMA DA MUTANE 20 NE SUKA MUTU A WANI HARIN KUDANCIN KADUNA

0
845

Daga Usman Nasidi

AKALLA sama da mutane 20 ne suka rasa rayukansu bayan wasu yan bindiga sun kai wani mummunan hari akan wasu al’ummomin kudancin Kaduna a ranar Litinin 20 ga watan Feburairun nan.

Shugaban hukumar Kaura na jihar Kaduna, Alex Iya ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace an kai hare haren ne kan al’ummomin Mifi da Ashim, tare da kashe mutane 14 a harin.

Sa’annan an sake kai wani hari a daren Lahadi 19 ga watan Feburairu kan al’ummar Bakin Kogi na karamar hukumar Jama’a, inda aka kashe mutane 7, yayin da da dama suka jikkata.

Shima dan majalisar jihar dake wakiltar mazabar Kaura Yakubu Bityong ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace maharani sun karkashe mutane da dama tare da babbaka gidaje da dama kafin isowar jami’an tsaro.

Bityong ya zayya sunayen wadanda aka kashe sun hada da: Chayuwai manti mai shekaru 73, Ezikiel kanwai dan shekara 23, Bridget aba mai shekara 61, Bridget samuila dake da shekaru 42, Samuila kuzamam dan shekara 47, Mathew daniel mai shekaru 37.

Kana da Edward mathew dan shekara 10, Omega mathew mai shekaru 8, Adam noga dan shekaru 46, Moses Ndong mai shekaru 68, Likita adam dan shekaru 12, Musa john mai shekaru 13, Mboi waje mai shekarau 14 da Fidelix kakah.

Allah ya kiyaye gaba, Ya kare mu, Ya bamu zaman lafiya a Najeriya da kwanciyar hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here