Daidaituwar Ra\’ayin Bangarori Biyu Na Gwamnati Na Kawo Ci gaba Matuka

  0
  731

  Jabiru A Hassan, Daga Kano.

  AN bayyana cewa  samun hadin kai tsakanin majalisu da bangaren zartaswa  yana kawo ci gaba mai kyau musamman a tsarin mulkin dimokuradiyya.
  Wannan tsokaci ya  fito ne daga dan majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar kananan hukumomin Bagwai da Shanono Alhaji Ali Ibrahim Isa Shanono a cikin tattaunawar su da wakilin mu, inda ya ce  idan akwai jituwa tsakanin bangaren majalisa da bangaren zartaswa ko shakka babu za\’a  sami ribar dimoluradiyya mai  yawa.
  Sannan ya  bayyana cewa yana dakyau a ci gaba da samun hadin kai da fahimtar juna tsakanin bangarorin guda biyu musamman ganin cewa tsarin mulkin dimokuradiyya ya kafu a wannan kasa  kuma an fahimci cewa mulkin dimokuradiyya shine mafi dacewa ga  kasashen duniya  domin  tabbatar da ci gaba mai kyau.
  Alhaji Ali Ibrahim  Isa Shanono ya kuma nunar da cewa ana cimma kyawawan nasarori tsakanin bangaren majalisu da gwamnati saboda haduwa da aka yi ana aiki tare kuma bisa tanade~tanaden da dokar kasa ta yi  kan hurumin kowane bangare, wanda hakan a cewarsa nan gaba kadan kasarnan zata bunkasa ta kowane fanni na zamantakewa.
  Dangane da kokarin da yake yi a mazabarsa kuwa, dan majalisar ya sanar da cewa daga lokacin da Allah ya bashi wakilcin kananan hukumomin Bagwai da Shanono ya  samar da aiyuka na raya kasa a wadanan yankuna guda biyu wadanda suka hada da karin  ajujuwa da sabunta makarantu da gina makarantu na isilamiyya da masallatai na juma\’a da gyare~gyaren su da  kuma  sauran aikace~aikace wadanda lokaci bazai bari  a bayyana su duka ba.
  Daga karshe, yayi godiya ta musamman ga gwamnatin jihar kano  bisa aiyukan da take aiwatarwa a fadin jihar duk da cewa ana fama da matsin tattalin arziki  da majalisar dokokin jihar  da su kan su al\’umar kananan hukumomin Bagwai da Shanono saboda  goyon baya da suke bashi domin ganin ya cimma nasarori masu yawa  a wakilcin sa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here