Ta Fitar Da Jadawalin Kakar Wasa Na Bana

  0
  904

  MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga kalaba

  HUKUMAR shirya gasar kwallon kafa ta kasa wato NNL ta ware ranar sha bakwai ga watan Maris matsayin ranara da za,a fara gasar rukunin kungiyoyin wasan kwallon kafa da ba su samu cancantar shiga gasar rukunin Premier ta kasa ban a shekarar 2016/2017 . Ta fitar da jadawalin yadda kowace kungiyoyi za su fafata .

  A sanarwar fara gasar ta watan gobe da hukumar ta sanar a taron da ta yi jiya Alhamis a Abuja  ta ce kungiyoyin da za su fafata a gasar sun hada da kungiyar  kwallon kafa ta Warri Wolves  da  Ikorodu United, Heartland FC wadda ta koma rukunin ‘yan dagaji a kakar wasan Premier da ta gabata .

  Haka nan kuma kungiyar kwallon kafa ta Giwa FC da ake takaddama kan shugaban ta ita kuma za ta jira ne har sai hukumar kwallon kafa ta nijeriya ta yanke hukuncin makomar kungiyar da maim ita idan za,a iya tunaw a shekarar da ta gabata ce aka kori kungiyar Giwa FC daga gasar Premier ta kasa saboda rashin jituwa da aka samu kan takarar mukamin shugaban cin  NFF da mai kungiyar ya yi da kuma wanda yake shugabanta a yanzu lamarin da har yanzu magana na gaban kotu.

   

  Ga yadda jadawalin gasar ya kama makon farko a watan goben 2016/2017 NNL Week 1 fixtures

  Rukunin  A

  Adamawa United da  Yobe Desert Stars.

  Bida Lions (Afe-Babalola) da  Sokoto United.

  FC Taraba da  Kwara United.

  FC Zamfara da  Kogi United.

  FRSC FC da  Kaduna United.

  Giwa FC da  Jigawa GS.

  Rukunin  B

  Bayelsa United da  Osun United.

  Abia Comets da  Warri Wolves.

  Akwa Starlets da  Unicem Rovers.

  AS Racine da  Papilo FC.

  Insurance FC da  My People FC.

  Crown FC da  Ikorodu United.

  Delta Force da  Heartland FC.

  First Bank da  Go Round FC.

  Dreams FC (Nnewi United) da  Gateway United.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here