WATA MATASHIYA TA JEFAR DA JIRIRINTA SABODA TA KASA GANE UBANSA

0
1008

Daga Usman Nasidi

AN kama wata matashiya mai shekaru 18 da ta bayyana sunanta a matsayin Timilehin Adeshina kwanan nan a lokacin da take yunkurin jefar da jaririn ta dan watanni 4 a duniya a karkashin gadar Oshodi a jihar Legas.

An saka jaririn a cikin wani jaka tsirara, sannan uwar tasa ta jefar da shi, wacce daga bisani wasu jami’an hukumar tsaro na jihar Lagas suka kama ta.

Da take bayanin dalilin ta na jefar da yaron, Timilehin wacce ta bar makaranta a aji biyu na sakandare, tace:

“Mahaifiya ta kore ni saboda na kasa sanin mutumin da yayi mun ciki. Nayi jima’I da mazaje daban-daban.”

Ta kuma bayyana cewa tana bacci da mazaje daban daban wadanda ke bata kudi, don kawai ta samu na al’amuran yau da kullun, tunda mahaifinta yam utu shekaru tara da suka wuce.

Tuni dai an mika Timilehin ga sashin kula da jin dadin matasa da ci gabansu na jihar Lagas

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here