Ya Kashe Mahaifinsa Dalilin Naira Dubu Daya

0
958

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

WANI yaro mai suna Ifeanyichukuw Ejeh da ke aji biyu na makarantar sakandare ta al’ummar Mbeke yankin karamar hukumar Abakaliki ,jihar Ebonyi ya kashe mahaifinsa, mai suna Micheal Ejeh,  har lahira da tabarya saboda Naira dubu daya.

Ana zargin Ifeanyichukwu,kamar yadda wakilinmu ya   samu labari an ce mahaiifn yaron Micheal yana barci ne a daki sai shi Ifeanyichukwu ya lababo da tabaryarsa a hannu ya dinga kwantara wa baban nasa a ka saboda an tambaye shi ina ya kai Naira dubu daya da aka aike shi ya sawowa iyalan su abinci shi kuma ashe wannan tambaya bata yi masa dadi ba sai ya yanke shawarar ya daukar wa kansa doka a hannu.

Da aka tambayi yaron dalilin da ya sanya ya yanke shawara ya kashe mahaifin nasa sai ya ce “ina karatu ne a gida sai wata zuciya ta raya min in je in kashe baban nawa daga baya kuma bayan na aikata hakan na dawo ina mai yin nadamar abin da na yi shaidan ne ya rinjaye ni”inji shi.

Mahaifiyar Ifeanyichukwu Mary Ejeh wadda ke gudanar da harkokin kasuwanci a Kalaba ta Jihar Kuros Riba ta sanarwa ‘yan jarida cewa “mijina bayan sun gama cacar baka da dan nasa saboda kudi Naira dubu da ya bashi ya je ya sayo abinci shi kuma ya batar da kudin wannan ta sanya shi musayar kalamai da baban nasa bayan sun gama ya hakura ya tafi ya kwanta yana barci ne yaron ya dauki tabarya ya same shi kwance a daki yana barci ya kwada masa tabarya har ya ci karfinsa ya kashe shi”in ji uwar yaron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here